Tashar Watsa Labarai Ta Gwamnatin Jihar Oyo Ta Kama Da Wuta

Tashar Watsa Labarai Ta Gwamnatin Jihar Oyo Ta Kama Da Wuta

  • Kafar watsa labarai mallakin gwamnatin jihar Oyo ta kama da wuta rigi-rigi kuma ana tsammanin wutar ta yi ɓanna
  • Bayanai sun nuna cewa gobarar ta fara tasowa daga ɗakin watsa shirye-shirye ana dab da fara shirin wasanni kwallo kai tsaye
  • Shugaban kafar watsa labaran ya bayyana illar da ibtila'in gobara ya tafka ranar Laraba

Oyo - Babbar tashar watsa labarai mallakin gwamnatin jihar Oyo ta kama da wuta a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Gobarar wacce ake zargin ta kama ne daga ɗakin watsa shirye-shirye, da yuwuwar ta yi kaca-kaca da muhimmin kayayyaki a ɗakin.

Gobara.
Tashar Watsa Labarai Ta Gwamnatin Jihar Oyo Ta Kama Da Wuta Hoto: Tribune
Asali: UGC

Wata majiya daga cikin ma'aikatan tashar watsa labaran ta bayyana cewa tuni aka sanar da hukumar kashe gobara kuma yanzu haka an duƙufa ƙoƙashin kashe wutar da shawo kan lamarin.

Kara karanta wannan

Jerin Jiga-Jigan Sanatocin PDP Guda 6 Waɗanda Ka Iya Neman Babban Mukami a Majalisar Dattawa

Tribune ta tattaro cewa lamarin ya faru da safiyar Alhamis kuma ya kawo cikas a harkokin watsa shirye-shirye yayin da ma'aikata suka yi iya bakin kokarinsu don dakile wutar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa gobarar ta kama ne rigi-rigi mintuna kaɗan bayan dawo da hasken wutar lantarki a ɗaya daga cikin dakunan gidan watsa labaran.

Da yake tabbatar da faruwar ibtila'in, shugaban hukumar watsa labarai, Prince Dotun Oyelade, ya ce gobarar ta fara ci ne mintuna kaɗan kafin fara shirin wasanni kai tsaye.

A kalamansa ya ce:

"Mun kusa ƙara shiga shirin wasanni kai tsaye, ba zato muka fahimci wurin canjin wuta ya kawo ba zato ba tsammani kuma ya ɗauke nan take."
"Mintuna kaɗan aka dawo da wuta kawai sai tartsatsin wuta wanda ya taba wayoyin ɗakin. Injiniyoyi sun yi kokarin shawo kan lamarin amma ya ci ƙarfinsu."

Kara karanta wannan

Cikon Zaben 2023: Tinubu Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Ruɗanin Zaben Gwamnan Adamawa

Ya ce a yanzu da yake magana ba zai iya bayyana yawan ɓarnar da gobarar ta yi amma zasu yi kokarin tattara komai su sanar zuwa gobe.

Yan Ta'adda Sun Halaka Magajin Gari, Sun Sace Mutane da Dama

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Halaka Magajin Gari, Sun Aikata Mummunar Ta'asa a Jihar Kaduna Cikin Azumi

Miyagun mahara sun kashe Dagaci kana suka tattara mutane da yawa suna tafi da su a Unguwan Ɗan Liman, karamar hukumar Birnin Gwari a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel