Zanga-zanga: FG ta ci tarar manyan gidajen talabiijin uku saboda kunyata gwamnati

Zanga-zanga: FG ta ci tarar manyan gidajen talabiijin uku saboda kunyata gwamnati

- An samu sabanin rahoto a tsakanin gwamnatin tarayya da kafafen yada labarai na gida da ketare a kan harbe-harbe a Lekki

- Kafafen yada labarai da dama sun nun wani faifan bidiyo da hotunan mutanen da ake zargin cewa sojoji sun budewa yayin zanga-zanga a Lekki

- Sai dai, gwamnatin tarayya ta musanta rahotannin kafafen yada labarai tare da bayyana cewa an kitsa hotuna da bidiyon da suka yada

Hukumar kula da kafafen watsa labarai na kasa (NBC) ta ci tarar gidan talabijin din AIT, Channels 24, da 'ARISE Television saboda nuna rashin kwarewa yayin yada zanga-zanagr ENDSARS.

Armstrong Idachaba, mukaddashin babban darektan NBC, ne ya sanar da hakan yayin taron da ya yi da manema labarai ranar Litinin a Abuja.

An ci tarar manyan gidajen talabijin din uku ne bayan zarginsu da yada wasu hotuna da bidiyon zanga-zanga da 'ba a tantancesu ba'.

NBC ta dade da gargadin kafafen yada labarai da ke Najeriya a kan su yi taka tsan-tsan da irin rahotannin da zasu yada yayin zanga-zanga domin gudun tunzura jama'a da kuma kunyata hukuma da sauran jama'a.

Zanga-zanga: FG ta ci tarar manyan gidajen talabiijin uku saboda kunyata gwamnati
Zanga-zanga: FG ta ci tarar manyan gidajen talabiijin uku saboda kunyata gwamnati
Asali: Twitter

An samu sabani a tsakanin gwamnatin tarayya da kafafen yada labarai na cikin gida da na waje a kan wasu rahotannin da aka yada yayin zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS.

Zanga-zangar, wacce aka fara da sunan ta lumana, ta koma rikici a jihohin da ta samu karbuwa, musamman a kudancin Najeriya.

A yayi da gwamnati ke zargin masu zanga-zanga da tayar da tarzoma, masu zanga-zanga na zargin gwamnati da yin amfani da wasu batagari domin bata sunan zanga-zangar ENDSARS da ke kara samun karbuwa a fadin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel