Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun fasa coci, sun yi awon gaba da masu ibada
- Kwana daya bayan jawabin gwamna, yan bindiga sun kai mumunar hari Kogi
- Gwamnan jihar yace jiharsa ta fi ko ina zaman lafiya a Najeriya
- Yan bindiga sun yi awon gaba da akalla mutum uku
Kogi - Yan bindiga sun kai har cocin Living Faith Church Worldwide dake unguwar Osara dake hanyar Lokoja zuwa Okene a karamar hukumar Adavi ta jihar Kogi.
Daily Trust ta ruwaito cewa yan bindigan sun yi awon gaba da mutum uku a cocin.
An tattaro cewa daga dirarsu cocin, yan bindigan suka fara harbin kan mai uwa da wabi domin tsoratar da mutane yayinda suke tafiya da wadanda suka sace.
Shugaban karamar hukumar Adavi, Joseph Omuya Salami, ta bakin mai magana da yawunsa, Habeeb Jamiu, ya tabbatar da cewa lallai an sace mutane uku.
Ya ziyarci wajen tare da DPOn yan sanda na Osaro domin tattauna yadda za'a ceto wadanda aka sace.
Bayan Shekaru 30, Jihar Mu Ta Fi Kowace Jiha Zaman Lafiya a Najeriya, Gwamna
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana jihar da yake jagoranta da wacce tafi kowace jiha zaman lafiya a Najeriya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Gwamnan Bello ya faɗi haka ne a yayin da yake jawabi ga mutanen jihar kai tsaye domin murnar cikar Kogi shekaru 30 da kafuwa.
Yace gwamnatinsa ta ɗauki lamarin tsaro, haɗin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali da matukar muhimmanci.
Bello yace an gida jihar Kogi a kan wasu manyan ginshikai uku, na farko shine toshe duk wata kafa ta handama da babakere da kuɗaɗen al'umma.
Asali: Legit.ng