Dattawan Arewa Sun Koka Akan Yadda Ake Kashe Yan Arewa A Kudu

Dattawan Arewa Sun Koka Akan Yadda Ake Kashe Yan Arewa A Kudu

  • Kungiyar Dattawan Arewa NEF, ta bayyana damuwarta kan yadda ake ta samun yawaitar kashe yan arewa a Kudu
  • Dr Hakeem Baba-Ahmed ya ce kisan yan kasar Nijar da aka yi a jihar Imo anyi shine bisa tunanin sun yan yankin Arewa ne
  • Kungiyar NEF ta yi kira gwamnati, alumma da jami’an tsaro suka kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin yan Arewa mazauna yankin kudu

Jihar Kaduna - Kungiyar Dattawan Arewa NEF, ta bayyana matukar damuwarta kan yadda ake ta samun yawaitar batanci da kashe-kashen yan Arewa a Kudancin Najeriya, musamman Kudu maso Gabas. Rahoton Daily Trust

Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na NEF, Dr Hakeem Baba-Ahmed ne ya bayyana matsayin kungiyar a cikin wata sanarwa a jiya.

Hakim
Dattawan Arewa Sun Koka Akan Yadda Ake Kashe Yan Arewa A Kudu FOTO Legit.NG
Asali: Facebook

Hukumar ta NEF ta ce, Kisan da aka yi wa ‘yan kasar Nijar kwanan nan a Jihar Imo, anyi shine bisa tunanin yan yankin Arewa ne,

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro : Mayakan Kuniyar Ansaru Sun Fara Auren Matan Yan Birnin Gwari

Wanda lamari ya shafi cin zarafi, kama mutane ba bisa ka’ida ba, hare-hare da kashe ‘yan Najeriya daga yankin Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ya kara da cewa da alama kungiyoyin da ke kai wa ‘yan Arewa hari suna samun kwarin guiwa ne daga shurun shuwagabanni da rashin daukar matakan da suka dace daga jami’an tsaro.

Kungiyar NEF ta sake jawo hankalin jama’a kan illolin da ke tattare da kara ta’azzara al’amura da tada hankali.

Daga karshe kungiyar ta bukaci gwamnati, al'umma da jami’an tsaro suka kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin yan Arewa mazauna yankin kudu

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Google Ta Hana IPOB Shiga Dandalin Ta

A wani labari kuma, Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, a ranar Alhamis ya roki kamfanin Google da ta hana mambobin kungiyar ‘yan asalin Biafra (IPOB) damar amfani da dandalinta. Rahoton Daily Trust

Kara karanta wannan

Ganduje zai cika alkawari, zai rattaba hannu domin rataye wanda ya kashe Hanifa

Da yake magana jiya a Abuja a lokacin da wata tawagar Google ta ziyarce shi, ya ce:

Asali: Legit.ng

Online view pixel