Dan sanda ya bindige mai babur, matasa sun bankawa ofishinsu wuta

Dan sanda ya bindige mai babur, matasa sun bankawa ofishinsu wuta

- Kimanin watanni biyu da zanga-zangar EndSARS, yan sanda na cigaba da kashe masu farin hula a Najeriya

- Matasa a jihar Anambra sun nuna bacin ransu kan kisan dan acaba ranar Laraba

Wasu matasa sun kona ofishin yan sanda Igboukwu dake karamar hukumar Aguata na jihar anambara, sakamakon harbin wani dan babur da jami'in dan sanda yayi a unguwar.

An tattaro cewa an samu sabani tsakanin yan sanda da masu sana'ar tukin babur sakamakon kwace baburan da aka yi saboda dokar hana tuka babur da dare a jihar.

Gwamnatin jihar ta bada umurnin daian hawa babur daga karfe 9 na dare.

A rahoton da Daily Trust ta koro, kakakin hukumar yan sandan Anambara, SP Haruna Mohammed, ya ce an samu sabani ne kuma hakan ya kai ga wani dan sanda ya harbi mai babur.

Sakamakon haka matasan suka bankawa ofishin yan sandan wuta.

A cewarsa, kwamishanan yan sandan jihar, CP John Abang, ya yi kira mutane su yi hakuri kuma ya bada umurnin damke dan sandan da yayi harbin.

Ya kara da cewa kwamishanan ya yi umurnin gudanar da bincike kan abubuwan da suka kai ga faruwan wannan abu kuma ya tabbatar da cewa "za'ayi adalci kuma za'a bayyanawa mutane sakamakon binciken."

KU KARANTA: Buhari ya bayar da umarnin bude iyakokin kan tudu guda hudu

Dan sanda ya bindige mai babur, matasa sun bankawa ofishinsu wuta
Dan sanda ya bindige mai babur, matasa sun bankawa ofishinsu wuta
Source: Instagram

KU DUBA: An bayyana sunaye da hotunan wasu cikin daliban da aka sace a Kankara

A makon da ya gabata, rikici ya barke a unguwar Rokpoku na birnin Fatakwal sakamakon bindige direban a-daidaita-sahu (Keke Napep).

Wannan abu da ya faru misalin karfe 7 na safiya Alhamis, a hanyar tashar jirgin sama ya haddasa rikici a yankin.

Wasu fusatattun matasa da abokan direban sun toshe hanyar suna zanga-zanga.

Wani mai idon shaida ya ce dan sandan ya kashe direban ne saboda ya ki bashi na goron N100 da ya bukata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel