Osinbajo Ya Bukaci 'Yan Najeriya Su Shiga Siyasa, Ya Fadi Amfanin Hakan
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi magana kan siyasa
- Farfesa Yemi Osinbajo ya buƙaci ƴan Najeriya musamman matasa da su sgiga a riƙa damawa da su cikin harkokin siyasa
- Ys ba su shawara da su tsaya su nemi ilminta kafin su tsunduma a cikinta domin kawo sauyin da ake buƙata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ba da shawarwari ga ƴan Najeriya musamman Kiristoci da matasa kan siyasa.
Farfesa Yemi Osinbajo ya buƙaci ƴan Najeriya, da su rika shiga harkokin siyasa domin amfani da ita a matsayin muhimmiyar hanya ta samar da shugabanci nagari da kuma kawo sauyi mai ɗorewa a cikin al’umma.

Asali: Twitter
Farfesa Osinbajo ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake gabatar da jawabi a taron tunawa da Daniel Taiwo Odukoya karo na biyu, wanda aka gudanar a cocin The Fountain of Life da ke Legas, cewar rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Osinbajo ya yi magana kan siyasa
A cikin jawabin nasa, Osinbajo ya ƙalubalanci yadda mutane da dama ke nuna ƙyama da yanke ƙauna daga siyasa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya nuna cewa duk da mummunan suna da siyasa ke da ita a halin yanzu, ita ce kaɗai hanya halastacciya ta samun jagoranci da tasiri a ƙasa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
"Siyasa ta samu mugun suna, ba kawai a Najeriya ba, har ma a duniya baki ɗaya. Amma gaskiyar magana ita ce, babu wata hanya ta tasiri ga ƙasa sai da shiga tsarin siyasa."
"Idan ba mu shiga wajen zaɓar shugabanni ba, ba mu da rawar gani wajen tsara manufofi ko shiga jam’iyyu, to babu hurumin da muke da shi na kuka idan abubuwan da suka biyo baya ba su yi daidai da ƙimar mu ba."
- Farfesa Yemi Osinbajo
Osinbajo ya jaddada cewa shiga siyasa ya kamata ya zama bisa fahimta, shirye-shiryen ilimi, da kuma tsantsar ɗabi’a da gaskiya.
Osinbajo ya ba matasa shawara
Yayin da yake magana kan matasan Najeriya da ke da burin shiga ofisoshin gwamnati, ya nuna cewa wajibi ne su kasance cikin shiri ta fuskar ilimi tare da fahimtar yadda shugabanci ke aiki.

Asali: Facebook
“Dole ne ku yi karatu. Ku fahimci yadda abubuwa ke tafiya. Ku karanta tarihin rayuwar shugabanni, ku fahimci tsarin lafiya, ilimi da tattalin arziƙi, musamman a cikin yanayin Afirika."
"Mutane da dama suna shiga siyasa ba tare da wani shiri ba, ba da ilimi ba, kuma a ƙarshe ba su cimma komai ba. Shugabanci na buƙatar fiye da haka."
- Farfesa Yemi Osinbajo
Batun ficewar Osinbajo daga APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Laolu Akande wanda yake kakakin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ne, ya yi magana kan raɗe-raɗin ubangidansa ya fice daga APC.
Laolu Akande ya bayyana cewa babu dalili da zai sanya tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya raba gari da jam'iyyar APC.
Raɗe-raɗin cewa Osinbajo ya fice daga APC ne bayan an daina ganinsa a wajen tarurrukan da suka shafi jam'iyyar tun bayan barinsa mulki a 2023.
Asali: Legit.ng