Jihar Katsina Ta Yi Babban Rashi a Ramadan, Gwamna Radda Ya Yi Shiga Jimami
- An yi rashi na daya daga cikin shugabannin hukumomin gwamnati a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma a Najeriya
- Shugaban hukumar samar da ruwan sha ta jihar Katsina, Injiniya Tukur Tingilin, ya yi bankwana da duniya sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da shi
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi alhini da jimami kan rasuwar ta shugaban hukumar samar da ruwan sha
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda, ya bayyana alhininsa game da rasuwar shugaban hukumar samar da ruwan sha ta jihar Katsina (KSWB), Tukur Tingilin.
Tukur Tingilin ya rasu ne sakamakon hatsarin mota da ya ritsa da shi a ranar Alhamis, 26 ga watan Fabrairun 2026.

Source: Facebook
Gwamnan Katsina ya yi ta'aziyyar rasuwar Tingilin
Babban sakataren yada labaran gwamnan Katsina, Ibrahim Kaulaha Mohammed, ya fitar sakon ta'aziyyar gwamnan a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a, 27 ga watan Fabrairun 2026.
A cikin saƙon ta’aziyyar, gwamnan ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga jihar, musamman a wannan lokaci da gwamnati ke ƙara ƙaimi wajen inganta samar da ruwan sha a faɗin kauyuka.
Gwamna Dikko Radda ya jinjina wa marigayi shugaban na hukumar samar da ruwan, inda ya bayyana jajircewarsa, kwarewarsa, da sadaukar da kansa ga aikin al’umma.
Rasuwar ta bar Gwamna Dikko Radda da jimami
"Gwamna Radda ya bayyana mutuwar a matsayin abin da ya girgiza shi, inda ya lura cewa shugabancin Injiya Tingilin a matsayin shugaban hukumar samar da ruwa ta jiha ya kasance abin koyo wajen hidimtawa jama’a ba tare da nuna son kai ba, har zuwa karshen rayuwarsa.”
“A ƙarƙashin jagorancinsa, an ƙarfafa tare da ci gaba ƙoƙarin tabbatar da cewa ruwa mai tsafta ya isa kowane gida a Katsina."
“Gwamnan ya samu natsuwar cewa Injiya Tingilin ya riga mu gidan gaskiya a matsayin Musulmi, kuma a cikin wannan watan mai alfarma na Ramadan.”
“Gwamna Radda, a madadin gwamnati da al’ummar jihar Katsina, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayin da kuma mutanen ƙaramar hukumar Malumfashi. Yana roƙon Allah Ya ba su juriya da ƙwarin gwiwar jure wannan babban rashi."
- Ibrahima Kaulaha Mohammed

Source: Facebook
An yi babban rashi
Wata mazauniyar Katsina, Aisha Kabir, ta bayyana cewa rasuwar marigayin babban rashi ne ga al'umma, inda ta yabe shi kan yawan kyautar da yake yi.
"Gaskiya wannan rasuwa babban rashi ne, muna fatan Allah Ya jikansa da rahama Ya kuma gafarta masa."
"Lokacin da muke karatu a Malumfashi yana yawan zuwa makarantarmu ya yi wa dalibai kyautar kudi. Mutum mai kirki matuka. An yabe shi da kulawa da marayu."
- Aisha Kabir
Karanta karin wasu labaran kan rashe-rashe
- Kannywood Ta Girgiza: Fitaccen Mai Shirya Fina Finan Hausa, Nura Sharu Ya Rasu
- Najeriya Ta Rasa Mahardacin Kur'ani a Madina, Shugaban Gwamnoni Ya Yi Ta'aziyya
- An Yi Rashi: Babban Mai Rike da Sarauta Kuma Surukin Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Rasu
- Duniya Labari: Sanata a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya, Ana Ta Rasa 'Yan Majalisa
Babban malami ya rasu a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa daya daga cikin malamai kuma shugaba a kungiyar Izalatul Bid'a Wa Ikamatus Sunnah (JIBWIS), reshen jihar Katsina, ya yi bankwana da duniya.
Kungiyar JIBWIS wacce aka fi sani da Izala ta tabbatar da rasuwar mataimakin shugaban ta na jihar Katsina I, Alhaji Sani Abubakar Daura.
Marigayin ya rasu ne a ranar Juma'a 25 ga watan Sha'aban 1447AH, wanda ya yi daidai da 13 ga watan Fabrairun 2026.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


