Sojoji sun kama ɗan aiken ISWAP da aka tura Legas ya siyo wa 'yan ta'adda kaya

Sojoji sun kama ɗan aiken ISWAP da aka tura Legas ya siyo wa 'yan ta'adda kaya

  • Sojojin Nigeria sun yi nasarar kama wani mutum da ake zargin dan aiken kungiyar ISWAP ne a jihar Ogun
  • Rundunar sojojin ta ce nagartattun bayannan sirri sun nuna cewa ISWAP ta aika mutumin zuwa Legas ne ya siyo mata wasu kayayyaki
  • Har wa yau, rundunar sojojin ta ce ta yi nasarar kama wani mutum da ake zargin mai satar danyen man fetur ne daga bututun NNPC

Hedkwatar tsaro ta sojojin Nigeria ta ce dakarun Operation AWATSE sun kama wani Ibrahim Musa da ake zargin dan kungiyar ta'addanci na ISWAP ne a yankin Sango Otta a jihar Ogun, The Cable ta ruwaito.

A yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi kan ayyukan rundunar daga ranar 18 zuwa 30 ga watan Yuni, Bernard Onyeuko, mukadashin direktan watsa labarai na sojoji ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin sintiri a unguwa Majidun a jihar inda aka kama Musa.

Dakarun Sojojin Nigeria
Dakarun Sojojin Nigeria. Hoto: The Nation
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Sunday Igboho ya nemi alfarma daga wurin Rundunar 'Yan Sanda gabanin gangamin Legas

A cewarsa, bayannan sirri ya nuna cewa an tura Musa zuwa Legas ne domin ya siyo wa kungiyar ta ISWAP wasu kayayyaki da suke amfani da su a Maiduguri, Daily Trust ta ruwaito.

Sojoji sun kama mai satar danyen man fetur daga bututun NNPC

Onyeuko ya ce dakarun sojojin sun kuma yi nasarar dakile bata garin da ke lalata bututun man fetur na kamfanin NNPC a Gaun, Wawa I da II a yankin Magbaro.

Ya ce a wani samamen sojojin, bisa bayyanan sirri sun kama wani Oyeshola Saheed da laifin satar danyen mai daga bututun NNPC da ke Alimosho.

"Amma ya ce wani Mr Akanbi ne ke daukan nauyin masu satar bakin man a yankin.
"An kama motocci da kayan satar man fetur din da bata garin ke amfani da su an kuma mika su ga hukumomin da suka dace don daukan mataki na gaba."

KU KARANTA: Ango ya fasa aure saboda abinci, ya kuma auri wata a ranar bikin

Ya ce babban hafsan tsaro, Lucky Irabor, tunda farko ya gana da janar din sojoji da suka yi murabus a yankin kudu maso kudu domin ganin yadda za a samu maslaha kan batun.

Ya ce ya gana da su ne da nufin gano ainihin dalilin yawaitar kallubalen tsaro a yankunan kasar nan domin ya amfani da gogewarsu da basira a matsayinsu na masu ruwa da tsaki.

A wani labarin, kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi takatsantsan da lamarin shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, rahoton Daily Sun.

A cewar kungiyar ta Arewa, shugaban na masu fafutikan kafa kasar Biafra yana da abokan hulda sosai a kasashen ketare.

Kungiyar ta yi wannan furucin ne yayin da ta ke martani kan sake kama shugaban na IPOB a ranar Talata 29 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel