Matakai 4 da Najeriya Ta Dauka bayan Fara Yakin Iran, Amurka da Isra'ila
Wannan rahoton ya kunshi wasu muhimman matakai da Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauka tun bayan fara yakin Iran da Amurka/isra'ila a ranar 28 ga Fabrairun 2026.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A ranar 28 ga watan Fabrairun 2026 aka fara gwabza yaki a Gabas ta Tsakiya bayan harin da Isra'ila/Amurka suka kai Iran.
Kasashe da dama a fadin duniya sun dauki matakai domin kare kan su daga rikicin da kuma inganta rayuwar 'yan kasa da tattalin arzikinsu.

Source: Facebook
A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu matakan da Gwamnatin Najeriya ta dauka domin inganta rayuwar 'yan kasarta da yakin ya shafa.
1. An dauki matakin kare 'yan Najeriya
Bayan fara yakin Iran, gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar gargadi ga ‘yan Najeriya da ke zaune a Iran da ƙasashen Gabas ta Tsakiya.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje, Kimiebi Ebienfa, ya sanya wa hannu, gwamnati ta ce tana sa ido sosai kan “yanayin da ke canzawa cikin sauri kuma mai haɗari” a yankin.

Source: Getty Images
Ma’aikatar ta ce an fitar da gargadin ne sakamakon tsananin tashin hankali da kuma yiwuwar ƙara tsanantar rikicin a yankin.
The Cable ta rahoto sanarwar ta ce:
“An shawarci dukkan ‘yan Najeriya da ke Iran da ƙasashen Gabas ta Tsakiya da abin ya shafa da su kasance cikin shiri sosai tare da kula da muhallinsu a kowane lokaci,”
2. An yi shirin ceto wadanda suka makale
Yayin da yakin ya yi kamari, Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba za ta iya gaggauta fitar da ‘yan Najeriya da suka makale a wasu sassan Gabas ta Tsakiya ba, sakamakon tsanantar rikicin da ya shafi Iran, Amurka da Isra'ila.
Jami’ai sun tabbatar da cewa duk da ana ci gaba da shirye-shiryen yiwuwar fitar da su, yanayin tsaro mai haɗari da kuma rikicewar zirga-zirgar sararin samaniya sun sanya ceto su cikin gaggawa ya zama mai wahala.

Source: Twitter
Rahoton Arise News ya nuna cewa wani jami’in gwamnati ya bayyana cewa ma’aikatar harkokin waje ta fara haɗa tsare-tsaren gaggawa tare da hukumomin da abin ya shafa domin ceto ‘yan Najeriya.
3. Batun warware matsalar makamashi
Yayin da yakin ya jefa duniya cikin matsalar makamashi, inda gas, fetur, man jirgin sama da sauransu suka tashi, Najeriya ta ce tana shirye ta warware matsalar.
Rahotanni sun nuna cewa Ministan yada labaran Najeriya, Mohammed Idris ne ya bayyana haka yayin wata hira da aka yi da shi a London.

Source: Twitter
Legit Hausa ta wallafa cewa ministan ya yi martani ne kan matakin da Iran ta dauka na toshe mashigar Hormuz da ake jigilar man fetur ta cikinta.
4. 'Yan sanda sun zauna cikin shiri
Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya ce hukumomin tsaro na sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a duniya da suka shafi yankin Gabas ta Tsakiya.
Jaridar Punch ta wallafa cewa ya yi magana ne yayin da zanga-zangar nuna goyon baya ga Iran da ta dauki hankalin jama’a a fadin ƙasar nan.

Source: Twitter
Disu ya ce bin diddigin al’amuran duniya wani bangare ne na dabarun aikin ‘yan sanda na amfani da bayanan sirri, musamman duba da cewa Najeriya na da kungiyoyin Musulmi daban-daban masu alaka da Gabas ta Tsakiya.
Legit ta tattauna da Musa
Wani magidanci a Najeriya, Malam Musa Muhammad ya bayyana cewa akwai bukatar Najeriya ta dauki mataki kan tsadar man fetur.
"Ana fama da matsalar man fetur, farashi ya tashi, ya kamata a ce an dauki matakin rage kudin shi."
'Wannan shi ne babban fatana a kan gwamnati."
Farashin mai ya karu a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa 'yan kasuwa na cigaba da kara farashin man fetur a Najeriya tun bayan fara yakin Iran da Amurka/Isra'ila.
Rahotanni sun bayyana cewa litar man fetur ta kai har N1,400 yayin da ake shirin shiga mako na hudu da fara yaki a Gabas ta Tsakiya.
Karin kudin man fetur da gas ya kara tsadar rayuwa a Najeriya, lamarin da ya kara jefa da yawa a cikin 'yan kasar cikin matsin tattalin arziki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


