Yadda Matar Aure Ta Shirya Makarkashiya, Ta So Tatsar Miliyoyi a Hannun Mijinta
- Wata matar aure ta shirya makarkashiyar karbar kudi masu kauri a hannun mijinta amma sai asirinta ya tonu
- Rundunar 'yan sandan jihar Edo ta bayyana cewa ta samu nasarar cafke matar bayan gudanar da bincike
- Matar auren dai ta hadi baki da wasu mutane ne domin sanyawa mijinta ya yi aman N5m ba tare da ya shirya ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Edo - Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta bayyana cewa ta kama wata mata mai suna Chioma Ezebie Adaniken kan zargin kitsa yin garkuwa da ita.
'Yan sandan sun cafke ta ne tare da wasu wadanda suka hada baki da ita, bisa zargin sun kitsa sace ta domin karbar N5m daga wajen mijinta.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakiyar jami’in hulda da jama’a ta rundunar, ASP Eno Ikoedem, ta fitar a ranar Talata, 4 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro ya gargadi Trump bayan barazanar kawo hari Najeriya, Buratai ya bada mafita
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan sanda sun yi caraf da matar aure
A cikin sanarwar, ta bayyana cewa bincike ya gano cewa matar ta hada baki da dan uwanta da wani matashi wajen shirya yin garkuwa da ita.
“Rundunar ‘yan sandan jihar Edo na sanar da jama’a cewa jami’anta na New Etete, birnin Benin, sun gano tare da kama wadanda ake zargi da kitsa yin garkuwa bayan cikakken bincike."
"A ranar 27 ga Oktoba, 2025, wani Paul Adaniken, mazaunin titin Limit Road, birnin Benin, ya kai rahoton cewa matarsa Chioma Success Ezebie (mai shekara 27) da ɗansu Andrea (mai shekara uku) sun bace bayan ya bar su a gida da safe ya tafi kasuwa."
"Daga bisani, an kira shi ta waya daga lambar da bai sani ba, inda aka shaida masa cewa an sace matarsa da ɗansa, inda aka bukaci ya biya N5m kafin a sake su.”
"Bayan haka, ‘yan sanda suka fara bincike, inda suka gano cewa dan uwan matar, Osita Godfrey (mai shekara 33), wanda da farko ana ganin yana taimakawa da bayanai, yana daya daga cikin masu hannu a lamarin."
“Bayan bincike, Godfrey ya amsa laifi kuma ya tona asirin matar, wacce ta yarda cewa ta hada baki da shi da wani Martins Chidozie (mai shekara 23) wajen shirya yin garkuwa da ita don ta damfari mijinta."
- ASP Eno Ikoedem

Source: Original
‘Yan sanda sun kwato kudin fansa
'Yan sanda sun ce sun kwato kudin fansa N5m da aka karba kuma sun mika lamarin ga sashen binciken manyan laifuffuka, don karin bincike da gurfanar da su a kotu.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Edo, CP Monday Agbonika, ya yaba da kokarin jami’an wajen gano wannan makirci, yana mai gargadin jama’a da su guji ayyukan da babu gaskiya a ciki.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da amfani da dabarun zamani wajen yaki da aikata laifuffuka a duk fadin jihar.
Jami'an 'yan sanda na neman Sowore
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Legas ta ayyana Omoyele Sowore a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.
Rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa tana neman tsohon dan takarar shugaban kasan ne saboda zargin tada zaune tsaye a Legas.
Hakan na zuwa ne bayan rundunar 'yan sandan ta ja kunnen Sowore kan shirya zanga-zanga sakamakon rusau din da gwamnatin jihar ta gudanar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

