Sojoji Sun Gwabza Faɗa da Ƴan Ta'addan Boko Haram a Borno, An Samu Asarar Rayuka

Sojoji Sun Gwabza Faɗa da Ƴan Ta'addan Boko Haram a Borno, An Samu Asarar Rayuka

  • Sojojin Operation Hadin Kai sun dakile harin Boko Haram/ISWAP a sansaninsu na Kangar, da ke Mallam Fatori
  • Rundunar sojoji ta kashe ‘yan ta’adda shida, ta kwato bindigogi, alburusai, da jirage marasa matuƙa guda hudu
  • Sojojin saman Najeriya da ta Jamhuriyyar Nijar sun kai hare-haren sama da suka tarwatsa ‘yan ta’adda da suka tsere

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Sojojin Operation Hadin Kai sun dakile wani mummunan hari da ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP suka kai wa sansaninsu a Borno.

An ruwaito cewa ƴan ta'addan sun farmaki sansanin sojojin FOB da ke Kangar, a garin Mallam Fatori, jihar Borno, da safiyar Talata, 4 ga Nuwamba, 2025.

Sojojin Najeriya sun gwabza fada da 'yan ta'adda a Borno
An kashe 'yan ta'adda yayin da suka kai hari sansanin sojoji a Borno. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Borno: Sojoji sun gwabza da 'yan ta'adda

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Lt. Col. Uba Sani , jami’in yaɗa labaran rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Gabas, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Yadda matar aure ta shirya makarkashiya, ta so tatsar miliyoyi a hannun mijinta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na asuba, inda ‘yan ta’addan suka yi amfani da jirage marasa matuka masu ɗauke da makamai wajen kai harin.

Sojojin sun nuna bajinta da kwarewa wajen kare sansanin, duk da tsananin harin da aka kai musu, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sanarwar Lt. Col. Uba Sani ta ce sojojin Sector 3 sun karfafa gwiwar sauran dakaru cikin salo na iya yaƙi, yayin da jiragen yaƙin ƙasar Nijar suka ba da taimako ta sama.

Sojojin sun yi nasarar murƙushe ƴan ta’adda

Bayan dogon lokaci ana musayar wuta, sai ‘yan ta’addan suka kasa jure irin barin wutar da sojoji suke yi, suka fara ranta wa a na-kare.

Sani ya bayyana cewa:

“‘Yan ta’addan sun rikice, kuma suka tsere zuwa cikin hanyoyin ruwa na Tumbuns, yayin da suka janye gawarwakin mutanensu da aka kashe.”

Binciken da aka yi bayan fafatawar ya tabbatar da cewa ‘yan ta’adda shida sun mutu, kuma sojojin sun kwato bindigogi biyar kirar AK-47, gidajen harsashi takwas, alburusai 258, RPG biyar, da jirage marasa matuka hudu, da ke dauke da makamai.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza da 'yan bindiga a Kano, an samu asarar rayuka

Haka kuma, an samu gurneti biyar, da wayar salula guda daya, wadda ake zargin tana dauke da bayanan sadarwa, da dai sauran kayayyaki.

Rundunar sojojin saman Najeriya tare da takwararta ta Nijar sun sake kai farmaki ga ‘yan ta’addan da suka tsere, inda suka kashe karin wasu a cikin daji da rafuffuka.

An kashe 'yan ta'adda da suka kai wa sojoji hari a Borno
Taswirar jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojojin da C-JTF sun jikkata a harin

A yayin da aka kora ‘yan ta’addan, wasu daga cikin sojojin da ke karkashin Operation Hadin Kai da kuma Civilian JTF sun samu raunuka kadan, in ji rahoton TVC News.

An ce an tura su asibitin rundunar haɗin gwiwar tsaro ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) don kulawa da lafiyarsu, amma Sanni ya ce suna cikin kyakkyawan yanayi.

Lt. Col. Sani ya kara da cewa rundunar MNJTF ta bayar da gudunmawar leƙen asiri da bayanan fikira da suka taimaka wa sojojin wajen gano ‘yan ta’addan da suka gudu.

Yadda sojoji suka ragargaji 'yan Boko Haram

A wani labarin, mun ruwaito cewa, dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) da ke yaki da ta’addanci a Arewa maso Gabas sun kashe ‘yan Boko Haram a Borno.

Kara karanta wannan

Mohammed Ma'aji: Abubuwa game da sojan da ya kitsa kifar da gwanatin Tinubu

Sojojin sun kashe 'yan ta'adda tara tare da kwato kuɗin fansa har N5m yayin wani sintiri a Magumeri da Gajiram, hedkwatar karamar hukumar Nganzai a jihar Borno.

Jami'in yada labarai na OPHK, Laftanar Sani Uba, ya bayyana cewa dakarun rundunar sun gudanar da aikin ne bayan samun sahihan bayanan sirri.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com