Trump: ECOWAS Ta Fadi Matsayarta kan Zargin Kisan Addini a Najeriya
- Kungiyar raya kasashen yammacin Afrika, ECOWAS ta musanta zargin kisan kare dangi kan wani addini a yammacin nahiyar
- ECOWAS ta ce irin waɗannan tuhumar na ƙoƙarin kawo rudani ne kawai da ta'azzara matsalolin tsaro da nahiyar ke fuskanta
- Kungiyar ta roƙi Majalisar Dinkin Duniya da sauran abokan hulɗa su goyi bayan ƙasashe wajen yaki da ta'addanci
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kungiyar raya kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta yi watsi da zarge-zarge da cewa ana kai kisan kare dangi ga wani rukuni na addini a yankin.
A wata sanarwa da ta fitar a daren Talata, kungiyar ta ce an yi amfani da irin waɗannan kalamai ne domin ɓata huldar ƙasashen yankin da kuma ƙara ta'azzara matsalolin tsaro.

Source: Getty Images
A sakon da ta wallafa a shafinta na X, ECOWAS ta bayyana cewa kan kowa da kowa, da suka hada da Musulmi, Kiristoci da mabiyan sauran addinai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ECOWAS ta yi watsi da kalaman Trump
Kungiyar ta tabbatar da cewa rahotanni masu zaman kansu sun nuna yadda 'yan ta'addan ke kaiwa duk wanda suka ga dama hari, ba tare da wariyar addini ba.
ECOWAS ta jaddada cewa tashin hankalin da ake samu na da alaƙa da ta'addanci ne tsagwaronsa, kuma babu la'akari dabambanci bisa jinsi, addini, kabila ko shekaru.

Source: Getty Images
Kungiyar ta ce ba daidai ba ne a ware wasu rukuni guda a kuma bayyana cewa ana yi masu kisankare dangi.
Sanarwar ta kuma yi kira ga duniya baki ɗaya da ta tsaya tare da ƙasashen yankin wajen yakar waɗannan ƙungiyoyin ta'addanci da ke zama barazana ga kowane al'umma.
Kungiyar ECOWAS ta nemi hadin kai
ECOWAS ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da duk abokan hulɗarta su tallafa wa 'yan ƙungiyar wajen yaki da ta'addanci.
Ta kuma bukace su da su ɗauki a matsayin ƙaryar duk wani zargi da ke nuni da cewa waɗannan ƙungiyoyi sun kebe wani rukuni wajen aikata masu ta'addanci.
Kungiyar ta nanata cewa ba za ta amince da waɗannan zarge-zargen masu haɗari wadanda ake amfani da su don ruguza zaman lafiya cikin al'umma da raunana haɗin kai ba.
A cikin sanarwar, ECOWAS ta ce akwai bukatar duniya ta tsaya tare da ƙasashen yammacin Afrika domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
Tuggar ya kare Najeriya daga zargin Trump
A baya, mun wallafa cewa Ministan harkokin wajen Najeriya ya ce gwamnati ba ta taɓa goyon bayan wariyar addini ko kisan addini ba, kuma ba za ta taɓa yin hakan ba.
Ministan ya bayyana hakan ne a birnin Berlin na ƙasar Jamus, yayin ganawa da takwaransa na Jamus, Johann Wadephul, inda ya ce gwamnati na bakin ƙoƙarinta.
Ya ce irin zarge-zargen da ake yi wa Najeriya na goyon bayan wariya ko kisan addini suna iya jefa kasar a cikin hadari tare da lalata sunanta a idon sauran ƙasashen duniya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

