China Ta Nunawa Trump Yatsa, Ta Gargadi Amurka kan Barazana ga Najeriya

China Ta Nunawa Trump Yatsa, Ta Gargadi Amurka kan Barazana ga Najeriya

  • Gwamnatin China ta gargadi Amurka da ta daina tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Najeriya bayan Donald Trump ya yi barazanar kaiwa kasar hari
  • Gwamnatin kasar China dake da alakar kasuwanci da kasar nan ta bayyana goyon baya ga gwamnatin Najeriya a matsayin ƙasa mai cikakken iko
  • Ta yi zargin cewa Amurka na amfani da addini da kare haƙƙin ɗan adam ne kawai don neman dalilin tsoma baki a cikin lamurran ƙasashe

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar China – Gwamnatin China ta bayyana goyon bayanta ga Najeriya a matsayin kasa mai cikakken iko dake tsaye da kafarta.

Ta yi gargadin cewa ba za ta lamunci kowace ƙasa ta yi amfani da addini ko kare haƙƙin ɗan adam a matsayin dalilin tsoma baki cikin harkokin wasu ƙasashe ba.

Kara karanta wannan

Najeriya da Amurka: Abdulsalami Abubakar ya fadi me ya ke ganin shi ne mafita

China ta nemi Amurka ta fitar harkar Najeriya
Donald Trump, Bola Ahmed Tinubu, Xi Jiping Hoto: officialABAT/Donald Trump/DonajurZhi
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Mao Ning, ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin Beijing ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

China ta goyi bayan Najeriya

Daily Post ta wallafa cewa China ta ce tana tare da gwamnatin Najeriya dake kokarin nemo hanyoyin ciyar da al'ummarta gaba.

Ta ce:

“A matsayinta na ƙasa mai cikakken haɗin gwiwar samar da ci gaba da Najeriya, China tana goyon bayan gwamnatin Najeriya da jama’arta wajen tafiya a tafarkin cigaban da ya dace da yanayin ƙasarsu.”

Ta ƙara da cewa China tana adawa da duk wani yunƙurin wata ƙasa da ke amfani da barazana ko takunkumi wajen matsa wa wata ƙasa lamba.

Ta jaddada cewa irin wannan salon takura da barazana da tsoratarwa ba ya taimakawa zaman lafiya da tsaron duniya.

China ta nanata goyon baya ga Najeriya

China ta kuma nanata cewa tana goyon bayan ƙoƙarin Najeriya wajen tabbatar da zaman lafiya, ta kuma yi kira ga Amurka da ta guji amfani da ƙarfi wajen gudanar da hulɗa da sauran ƙasashe.

Kara karanta wannan

Kiristoci: Peter Obi ya fadi matsayarsa kan yunkurin Amurka na kawo farmaki Najeriya

China ta ce Najeriya na bakin kokarinta
Hoton Bola Ahmed Tinubu da Xi Jiping na China Hoto: Ajuri Ngelale
Source: Twitter

Ta ce:

“Muna kira ga Amurka ta koma hanyar haɗin kai ta doka da diflomasiyya domin kauce wa matakan da za su iya kawo tashin hankali a yankin.”

Wannan martani na China ya biyo bayan kalaman shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya umarci ma’aikatar yaƙin Amurka da ta fara shirye-shiryen kai farmaki a Najeriya.

Trump ya ce ya bayar da umarnin ne saboda zargin cewa ana kashe kiristoci saboda addininsu, kuma ya dorawa kansa da Amurka nauyin kare su.

An gano dalilin Trump na takurawa Najeriya

A baya, mun wallafa cewa wani masanin siyasa, Farfesa Jibrin Ibrahim ya ce barazanar Donald Trump na kai hari ga Najeriya kan batun kisan kiristoci ba komai ba ne face siyasa.

Ya bayyana cewa Shugaban Amurka Donald Trump na takaicin yadda Najeriya ta yi kusanci sosai da kasar China ta fuskoki da dama, musammam masana'antu da ma'adanai.

Kara karanta wannan

'Ta sama ko ta kasa,' Donald Trump ya fadi shirinsa kan kai hare hare Najeriya

Farfesa Jibrin ya kara da cewa wannan barazana ba don kaunar kiristoci aka yi shi ba, illa kawai siyasar duniya da ya ke amfani da ita wajen bayyana takaicinsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng