Babbar Magana: Rigima Ta Kaure a Zaman Majalisar Wakilan Tarayya, An Yi Musayar Yawu

Babbar Magana: Rigima Ta Kaure a Zaman Majalisar Wakilan Tarayya, An Yi Musayar Yawu

  • Yan Majalisa sun yi muhawara mai zafi a zaman Majalisa Wakilai na yau Talata, 4 ga watan Nuwamba, 2025
  • Lamarin ya faru ne yayin tattaunawa kan kudirin da ya nemi gudanar da bincike kan zargin sayar da wasu kadadarin gwamnati a Legas
  • Da rikicin ya nemi gagara, mataimaki kakakin Majalisar, Hon. Benjamin Kalu ya bada umarnin komawa zaman sirri domin samun mafita

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Rikici da hayaniya sun barke a zaman Majalisar Wakilai ta tarayya a ranar Talata kan zargin sayar da kayan gwamnati ba bisa ka'ida ba a kasuwar duniya ta Legas.

Kara karanta wannan

CAN: Martanin Kiristocin Arewa bisa barazanar Trump na kawo farmaki a Najeriya

‘Yan majalisa sun yi muhawara mai zafi kan wane kwamiti ya dace ya gudanar da bincike kan zargin sayar da kadarorin a kasuwar baje kojin jihar Legas.

Majalisar Wakilan Tarayya.
Hoton daya daga cikin zaman Majalisar Wakilai ta Tarayya a Abuja Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

Abin da ya kawo rikici a Majalisa

Daily Trust ta rahoto cewa ce-ce-ku-cen ya samo asali ne daga kudirin gaggawa da dan majalisa, Hon. Ademorin Kuye ya gabatar a zaman yau Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Kuye ya bukaci majalisar ta gudanar da bincike kan zargin sayar da kadarorin gwamnati a wurin baje kolin, inda ya nemi Kwamiti Kula Kadarorin Gwamnatin ya jagoranci binciken.

Sai dai Shugaban Kwamiti Ka’idoji da Harkokin Majalisa, Francis Waive, ya tashi ya kawo ra'ayinsa cewa al’amarin ya shafi harkokin kasuwanci, don haka ya kamata a mika shi ga Kwamitin Kasuwanci.

Wannan ya haddasa muhawara mai zafi tsakanin ‘yan majalisa, yayin da wasu ke ganin kwamitin kula da kadarorin gwamnati ya dace, wasu kuma suka dage cewa kwamitin kusuwanci ke da hurumin binciken.

Yan Majlisa sun yi musayar yawu

Hon. Yusuf Adamu Gagdi (APC, Filato) ya dage cewa bisa Order 109, Rule 1 da 2 na dokokin majalisar, kwamitin kadarorin gwamnati ke da hurumin duba kowace irin kadara ciki har da wadanda ke wajen kasar.

Kara karanta wannan

An bai wa Tinubu hanyoyin yiwa Trump martani bayan barazana ga Najeriya

"Filin baje kolin kasuwanci mallakar gwamnatin tarayya ne, don haka yana karkashin kwamitin kadarorin gwamnati,” in ji Gagdi.

Amma Hon Mark Esset (PDP, Akwa Ibom) ya saba masa, yana mai cewa filin baje koli wata hanya ce ta kasuwanci, ba wai kadarar gwamnati da ake sayarwa ba.

“Kasuwar baje koli ba kadarar gwamnati ba ce. A cikin dokokin majalisa, an sanya ta a karkashin aikin Kwamitin Kasuwanci,” in ji Esset.

Wane mataki shugaban Majalisa ya dauka?

Yayin da hayaniya ta yi kamari, Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu, wanda ke jagorantar zaman, ya shiga tsakani don kwantar da hankalin abokan aikinsa.

Ya bayyana cewa abin da ke gaban majalisa shi ne bincike kan yadda aka raba wuraren gudanar da baje kolin, ba harkar kasuwanci kai tsaye ba.

Bayan tattaunawa mai tsawo, Kalu ya yanke shawarar kafa kwamitin wucin gadi mai kunshe da mambobin kwamitin kula da kadarori da na kasuwanci don gudanar da binciken tare.

Majalisar Wakilai.
Hoton zaman Majalisar Wakilai karkashin jagorancin Hon. Benjamin Kalu Hoto: @MukhtarShagaya
Source: Twitter

Duk da haka, sai da wasu ‘yan majalisa sun nuna adawa da wannan mataki, bisa haka, aka jefa kuri’a kan lamarin, ’yan majalisa da dama sun kada kuri’ar “a’a”, wanda ya haddasa karin hayaniya .

Kara karanta wannan

Kama dalibin jami'ar da ya soki gwamna a Facebook ya fara tayar da kura a jihar Neja

Domin kwantar da hankali, Mataimakin Kakakin Majalisa ya umarci a koma zaman sirri domin tattauna matsalar a cikin gida, kamar yadda Bussiness Day ta kawo.

Majalisa ta amince da bukatar Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar Wakilai ta amince da bukatar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na karbo bashin Dala biliyan 2.3 daga kasashen waje.

Majalisar ta amince da bukatar ciyo bashin ne bayan karbar rahoton kwamitin tallafi da harkokin bashi.

Rahoton ya nemi majalisa ta amince gwamnatin tarayya ta aiwatar da shirin nemo rance da kuma sake biyan tsofaffin bashin da aka tanada a cikin Kasafin Kudin 2025.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262