Majalisar Wakilai Ta Amince Tinubu Ya Karbo Bashin Dala Biliyan 2.3 daga Ketare
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kara ciyo bashi daga kasashen ketare domin cike gibin kasafin kudin 2025
- Hakan dai ya biyo bayan amincewar da Majalisar Wakilai ta yi da batun karbo bashin Dala biliyan 2.3 daga kasashen ketare
- Ta ce za a yi amfani da kudin wajen biyan bashin Eurobond, wanda wa'adinsa zai kare a watan Nuwamba, 2025 don kare mutuncin Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Najeriya - Majalisar Wakilai ta kasa ta amince da bukatar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na karbo bashin Dala biliyan 2.3 daga kasashen waje.
Shugaba Bola Tinubu ya nemi izinin dauko wannan rance ne domin rage gibin kasafin kudin 2025 da kuma biyan wasu tsofaffin bashin Eurobond na Najeriya.

Source: Facebook
Premium Times ta tattaro cewa Majalisar ta amince da bukatar ciyo bashin ne bayan karbar rahoton kwamitin tallafi da harkokin bashi a zaman yau Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban Kwamitin Majalisa kan Tallafi, Rance da Gudanar da Bashi, Hon. Abubakar Nalaraba (APC, Nasarawa) ne ya gabatar da rahoton a zauren majalisar.
Rahoton ya nemi majalisa ta amince gwamnatin tarayya ta aiwatar da shirin nemo rance da kuma sake biyan tsofaffin bashin da aka tanada a cikin Kasafin Kudin 2025.
Shawarwarin da kwamitin ya ba Majalisa
Kwamitin ya shawarci Majalisar Wakilai da ta amince da karbo sabon bashi daga waje na Naira tiriliyan 1.84 (kimanin Dala biliyan 1.23) domin cike gibin kasafin kuidin shekarar 2025.
Haka kuma, ya bukaci majalisar da ta amince da biyan bashin Eurobond na Dala biliyan 1.12 (Wanda wa'adinsa ke karewa a watan Nuwamba 2025) domin gujewa rashin biyan bashi da kare mutuncin Najeriya a kasuwar bashi ta duniya.

Kara karanta wannan
Bayan karbar bukatar Tinubu, majalisa ta sa lokacin tantance sababbin hafsoshin tsaro
Bayan gabatar da rahoton, Majalisa ta tattauna kan lamarin tare da yanke hukuncin karshe kan bukatar shugaban kasa.
Yadda Majalisa ta amince da ciyo bashin
A yayin tattaunawa, Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye, Hon. Abdullahi Halims (APC, Kogi), ya nemi kawo cikas, inda ya roki a jinkirta amincewa da rahoton domin a kara nazari kan shirin neman bashin.
Sai dai Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, wanda ya jagoranci zaman, ya nuna rashin jin daɗinsa da wannan shawara, yana cewa:
“Ban ji daɗin wannan magana a kan batun da ba a kai ga cimma matsaya ba. Ina roƙonka da ka janye ta.”

Source: Twitter
Daga nan Hon. Abdullahi Halims ya janye kokensa, kuma majalisar ta ci gaba da amincewa da shawarwarin kwamitin daya bayan daya, kamar yadda Punch ta rahoto.
A ƙarshe, Majalisar ta amince da rahoton gaba ɗaya, kuma ta ba da cikakken izini ga gwamnatin tarayya ta karbo wannan bashin daga kasashen waje.
Majalisa na shirin gyara dokar EFCC
A baya, kun ji cewa majalisar wakilai ta fara karatu kan kudirin da ke neman gyara dokar kafa EFCC domin bai wa hukumar 'yancin cin gashin kanta.
Dan majalisar wakilai daga jihar Filato, Yusuf Gagdi, ke ya jagoranci tattaunawa kan muhimman dalilan da kudirin ya kunsa.
Daya daga cikin muhimman abubuwan da kudirin ya kunsa shi ne rage ikon shugaban kasa wajen cire shugaban hukumar EFCC.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
