An Bai wa Tinubu Hanyoyin Yiwa Trump Martani bayan Barazana ga Najeriya

An Bai wa Tinubu Hanyoyin Yiwa Trump Martani bayan Barazana ga Najeriya

  • Wani 'dan Najeriya mazaunin Amurka, Baba Adam, ya rubuto wasika ga Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a kan barazanar Donald Trump
  • Shugaban kasar Amurka ya yi wa Najeriya barazanar kawo mata hari ta sama ko ta kasa kwanaki kadan bayan zargin kisan kiristoci a kasar
  • Baba Adam, wanda 'dan gwagwarmaya ne ya shawarci Bola Ahmed Tinubu a kan matakan da ya dace ya dauka bayan wannan barazana

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Wani dan Najeriya da ke zaune a Amurka, Baba Adam, ya rubuta wasikai ga Shugaba Bola Tinubu da wasu manyan jami’an gwamnati.

A cikin wasikar, ya bayar da shawarwari a kan yadda ya kamata Shugaba Tinubu ya yi martani da barazanar da Trump ya yiwa Najeriya, kasa mai cikakken iko.

Kara karanta wannan

"Zan goyi bayan Trump": Wike ya yi magana kan barazanar shugaban Amurka

Wike ya karyata zargin Trump a Najeriya
Shugaban Amurka, Donald Trump, Bola Tinubu Hoto: Donald J Trump/Bayo Onanuga
Source: Getty Images

Premium Times ta wallafa cewa Baba Adam ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta ɗauki matakin gaggawa domin kare martabar Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shawarawarin da aka bai wa Tinubu kan Trump

A cikin wasikar da ya aike ta imel a ranar Lahadi, Baba Adam ya ce kalaman da Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social a ranar 1 ga Nuwamba suna nuna irin tsohuwar siyasar tursasawa.

Ya bayyana cewa wannan tsari ya saba da dokar kasa da kasa, kuma bai kamata gwamnatin Najeriya ta yi gum a kan batun ba.

An shawarci Tinubu ya tsaya da kafarsa
Hoton Shugaban Najeriya, Bola Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Baba Adam ya bayyana cewa ya kamata gwamnatin Tinubu ta kira jakadan Amurka nan take domin ta mika takardar ƙorafi.

Ya kara da cewa idan lamarin ya zafafa, Najeriya ta yanke hulɗa da Amurka, domin a kalamasa, dole ne a kare mutunci da martanar Najeriya.

An nemi kai Trump gaban Majalisar Dinkin Duniya

Baba Adam ya kuma shawarci gwamnati da ta kai ƙarar Amurka zuwa Majalisar Ɗinkin Duniya, domin tabbatar da ikon Najeriya a matsayin ƙasa mai cikakken ‘yanci.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisa a Amurka ya taɓo Kwankwaso kan Shari'a bayan martani ga Trump

Haka kuma, ya bukaci a kira taron gaggawa na ECOWAS da Tarayyar Afrika, a bayyana cewa duk wani hari kan Najeriya hari ne kan Afrika baki ɗaya.

A cewarsa, ya kamata Majalisar Dokoki ta Najeriya ta zartar da ƙuduri da ke sukar barazanar Trump da kuma tabbatar da cikakken ikon ƙasar.

Baba Adam ya ce lokaci ya yi da Tinubu zai gwada amincin ƙawayen Najeriya a Turai, musamman Faransa, domin ganin ko za su tsaya tare da Najeriya idan rikici ya taso.

Kalaman Trump sun fusata Wike

A baya, mun wallafa cewa Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya fito fili ya yi tir da yadda wasu ‘yan adawa ke amfani da batun zargin kisan kiristoci a Najeriya.

Ya bayyana cewa a matsayinsa na kirista a gwamnati mai ci, ya san cewa akwai manyan jami'a kuma kiristoci, saboda haka babu maganar kisan kare dangi ga mabiya wani addini.

Wike ya yi tir da wasu 'yan adawa da ya ce suna amfani da batun domin kara fito da kansu, saboda sun rasa yadda za su yi da gwamnati mai ci a karkashin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Kiristoci: Peter Obi ya fadi matsayarsa kan yunkurin Amurka na kawo farmaki Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng