Yadda Sanata Natasha Ta Sauke Wa Jami'an NIS Ruwan 'Masifa' a Filin Jirgin Sama a Abuja
- An fafata tsakanin jami'an Hukumar NIS da Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan
- Sanata Natasha ta je filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja yau Talata da nufin tafiya hutun mako guda a kasar waje
- Sanatar Kogi, Natasha ta bayyana cewa bayan shafe tsawon lokaci ana takaddama, hukumar NIS ta maida mata da fasfo dinta
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - An yi wata yar dirama da hatsaniya a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, a ranar Talata, lokacin da jami’an Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS) suka kwace fasfon Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Sanatar, mai wakiltar mazabar Kogi ta Tsakiya ta tunkari jami'an NIS kai tsaye domin jin dalilin karbe mata fasfo, lamarin da ya sa aka dawo mata da shi daga karshe.

Source: Original
Natasha ta yi bidiyo kai tsaye a shafinta na Facebook, inda ta ce lamarin ya faru ne yayin da za ta fita ƙasar waje bayan kammala taron bikin cika shekara biyu a ofis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Natasha ta soki jami'an NIS
Rahotanni sun nuna cewa jami'an NIS sun karbe mata fasfo a lokacin da take shirin hawa jirgi, amma Sanata Natasha ta nuna sam hakan ba za ta yiwu ba domin babu laifin da ta yi.
A cikin bidiyon da ya karade kafafen sada zumunta, Natasha ta ce:
“A kan me za ku riƙe da fasfona? ’Yan Najeriya, ku saurare ni. Na kammala bikin cika shekara biyu a majalisa kuma na yanke shawarar yin hutu na mako guda.
"Amma ga shi yanzu jami’an NIS sun ƙi su ba ni fasfona. Haka aka yi min a baya, inda aka ce umarnin shugaban majalisa, Godswill Akpabio ne cewa kada a bar ni na fita saboda wai ina tozarta Najeriya a kafafen waje.”
Sanata Natasha ta ce wannan cin zarafi ne kuma ta nemi a daina yin hakan, tana mai cewa babu wani jami'i da ke da ikon rike mata fasfo haka kurum.
Yadda Natasha ta tayar da hayaniya
Lokacin da Natasha ta tayar da hayaniya a filin jirgin, wata jami’a mace da ke kan bakin aiki ta yi kokarin lallashinta da kalamar 'ki yi hakuri," amma Natasha ta nuna sam ba za ta hakura ba.
“Kada ki ba ni hakuri, ki bani fasfona kawai. Na tsaya a nan tsawon mintuna 20," in ji ta.
Natasha ta ƙara da cewa a baya da aka kama fasfonta, sai da ta kira wani babban mutum kafin aka sake mata, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Source: Facebook
Ta kuma bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a dakatar da duk wasu shari’o’in siyasa da aka kitsa mata.
Bayan tsawon lokaci ana takaddama tsakaninsu, wani jami’in NIS ya iso wurin tare da kawo mata fasfon nata, wanda ya damƙa mata kafin ta bar wurin.
Natasha ta yi wa sanatoci uzuri
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Natasha Akpoti ta yi wa abokan aikinta sanatoci uzuri bisa gaza tsaya mata a dambarwarta da shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

Kara karanta wannan
Kama dalibin jami'ar da ya soki gwamna a Facebook ya fara tayar da kura a jihar Neja
Ta ce tsoron tsangwama da siyasa ne ya sa wasu abokan aikinta a majalisa suka kasa bayyana goyon bayansu gare ta lokacin da aka dakatar da ita.
Sanata Natasha ta bayyana cewa wasu sanatocin sun nuna tausayi ta hanyar kiran waya da ziyara amma sun gaza nuna hakan a fili.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

