Natasha Ta Yiwa Sanatoci Uziri, Ta Ce Tsoro Ya Hana Su Tsaya Mata a Majalisa
- Natasha Akpoti-Uduaghan ta bayyana dalilin da ya jawo wadansu 'yan majalisa suka ki tsaya mata a dambarwarta da Godswill Akpabio
- Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta shiga matsala bayan dambarwarta da Shugaban Majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio
- Lamarin ya kai har an dakatar da ita na tsawon watanni shida, kuma a wannan lokaci, ba a samu yan majalisar da suka ja daga da Akpabio kan batun sosai ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta tsakiya, ta bayyana cewa ta san dalilin da ya hana wasu Sanatoci su tsaya mata a dambarwarta da Godswill Akpabio.
A cewarta, tsoron tsangwama da siyasa ne ya sa wasu abokan aikinta a majalisa suka kasa bayyana goyon baya gare ta lokacin da aka dakatar da ita daga majalisar dattawa.

Kara karanta wannan
Yadda Sanata Natasha ta sauke wa jami'an NIS ruwan 'masifa' a filin jirgin sama a Abuja

Source: Twitter
TVC news ta wallafa cewa Natasha ta bayyana hakan ne a garin Okene, Jihar Kogi, a ranar Lahadi yayin kaddamar da sabon kasuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Natasha ta magantu kan abokan aikinta
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Sanata Natasha ta bayyana cewa wasu sanatocin sun nuna mata tausayi ta hanyar kiran waya da ziyara.
Ta kara da cewa amma sun ki bayyana hakan a fili saboda tsoron abin da zai biyo baya, musamman ta fuskar siyasarsu.
A kalamanta:
“Lokacin da jami’in gwamnati ke fuskantar ƙalubale, mutane kan nesanta kansu da shi. Ko da suna tausaya maka, suna tsoron su nuna hakan a fili saboda gudun zargi ko tsangwama."
“Da yawa daga cikin sanatoci sun goyi bayana, amma ba su iya bayyana hakan a bainar jama’a ba. Ban ji haushin hakan ba."
Yadda dakatar da Natasha ta jawo matsala
Natasha ta bayyana cewa dakatarwar da aka yi mata ta yi illa ga wasu ‘yan kwangila da ke kula da ayyukan mazabarta, inda aka samu jinkiri.

Source: Facebook
Ta ce:
“Kudirin kasafin 2025 ya fara aiki ne a lokacin da ake dakatar da ni ba bisa ka’ida ba."
Ta ce wasu ‘yan kwangila sun wahala wajen samun takardun kwangila saboda ayyukan da aka ware ga Kogi ta tsakiya, kuma akwai siyasa a cikin tsarin bayar da kwangila da fara ginin ayyuka.
Duk da wannan, ta ce ta ci gaba da maida hankali wajen hidimar mazabarta ba tare da ta bari wahalarta ta shafi su ba.
Natasha ta caccaki Akpabio
A baya, mun wallafa cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta bayyana cewa jami’an hukumar shige da fice sun kwace mata fasfo a filin jirgi yayin da take shirin tafiya ƙasa da ƙasa.
Ta bayyana haka ne a lokacin da ta rika daukar bidiyo kai tsaye, tana sanar da duniya cewa wani jami'i ya tabbatar mata da cewa Sanata Godswill Akpabio ne ya bayar da umarnin.
A cewar ta, wannan ba shi ne karon farko da Akpabio ke bayar da umarni a kwace mata fasfo, kuma ko a baya, sai da wani babba a kasar nan ya saka baki kafin a maida mata fasfon.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
