Zargin Kisan Kiristoci: Wike Ya Zargi 'Yan Adawa da Wuce Gona da Iri wurin Yada Karya
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce zargin hallaka Kiristoci karkashin mulkin Bola Tinubu tsantsar siyasa ce
- Tsohon gwamnan Rivers ya zargin jam'iyyun adawa da wuce gona da iri inda su ka yada cewa ana yi wa kiristocin kasar nan kisan kare dangi
- Ya yi martanin ne bayan tsohon Amurka Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar matakan soja kan Najeriya kan zargin kashe kiristoci
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ƙaryata zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.
Ya ce a matsayinsa na kirista, wanda duka iyalansa kiristoci ne, yana da tabbacin cewa babu kamshin gaskiya a labarin da ake yadawa a yanzu.

Source: Facebook
A cikin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels Television, Wike ya ce wannan lamari siyasa ce da ta wuce gona da iri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya karyata zancen kisan kiristocin Najeriya
The Cable ta wallafa cewa Nyesom Wike ya kara da cewa babu wani shugaba a Najeriya da zai yi murna da kashe-kashe a kowane yanki.
Ya kuma ya jaddada cewa manyan jami’an tsaro da lauyoyi kamar shugaban ‘yan sanda, daraktan ƙasa na hukumar DSS da shugaban sojoji duka kiristoci ne.
Wike ya kara da cewa wannan na nufin ikirarin da Trump ya yi ba shi da tushe domin babu yadda za a yi gwamnati ta zura ido ana kashe kiristoci saboda addininsu.
Ya ce a matsayinsa na kirista, ya sani cewa gwamnatin Najeriya ba za ta lamunci a rika yi wa kiristoci kisan kare dangi ba.
A kalaman Wike:
“Ni Kirista ne. Mahaifina fasto ne; dangina duk Kiristoci ne. … Wannan zargi ya shafi ni a matsayina na Kirista cewa a cikin gwamnati da nake yiwa aiki za a yi zargin cewa tana tallafawa hallaka Kiristoci.”
Wike ya dura a kan 'yan adawa
Wike ya yi zargin 'yan adawa suna amfani da wannan dama ta batun kisan kiristoci domin su tallata kansu wajen kara zafafa adawa da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Source: Facebook
Ya ce yan adawa na ganin cewa bai kamata su bar gwamnati haka kawai ba, shi ne suka bullo da maganganun da za su raba kasa domin jefa ta a cikin matsala.
Wike ya yi zargin ana amfani da wannan batu wajen faɗaɗa bambanci tsakanin kiristoci da Musulmi, wanda zai iya zama barazana ga zaman lafiya.
Zargin kisan kiristoci: Shehu Sani ya soki Trump
A baya, mun wallafa cewa kalaman shugaban Amurka, Donald Trump ba su yi wa Sanata Shehu Sani dadi, inda ya yi zazzafan martani da aka kira Najeriya wulakantacciyar kasa.
Tsohon Sanata, Shehu Sani ya ƙaryata cewa Najeriya wata “wulakantacciyar kasa ce, inda ya nanata cewa kasarsa ba za ta taba zama abin da Donald Trump ya kira ta ba.
Shehu Sani ya jaddada cewa matsayinsa shi ne ya zama ɗaya daga cikin waɗanda suka nuna adawa game da ƙowane irin farmakin soja da Trump ya ce zai iya kawo wa Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


