'Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'an Tsaro yayin Wani Kazamin Hari a Zamfara
- An shiga jimami a jihar Zamfara bayan 'yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna yayin da suke gudanar da aikin sintiri
- Miyagun 'yan bindigan sun hallaka jami'an tsaron bayan sun shammace su inda suka bude musu wuta
- Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi ta'aziyyar rasuwar jami'an tsaron tare da yi musu addu'ar samun rahama a wajen Allah Madaudakin Sarki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan hari inda suka kashe jami'an tsaro a jihar Zamfara.
'Yan bindigan sun hallaka ‘yan sanda biyar da jami’an rundunar Askarawa guda uku yayin da suke sintiri a hanyar Gusau–Funtua da ke cikin karamar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.

Source: Facebook
Wani mazaunin yankin, Ya’u Musa, ya shaida wa The Punch cewa harin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis, 16 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan
Zargin bata sunan hadimin Gwamna Abba: 'Yan sanda sun yi magana kan tsare dan jarida
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda 'yan bindiga suka kashe jami'an tsaro
Harin ya auku ne a lokacin da jami’an tsaron ke sintiri a kusa da kauyen Gidan-Giye, kimanin kilomita kadan daga garin Tsafe, hedikwatar karamar hukumar.
“Suna kan hanya ne zuwa Gidan-Giye lokacin da ‘yan bindigar suka fito daga boyayyen wurinsu suka bude musu wuta."
- Ya'u Musa
A cewarsa, dukkan jami’an da ke cikin motar sun mutu nan take bayan harin.
Ya kara da cewa akwai yiwuwar ‘yan bindigan sun samu bayanai daga wasu masu ba su labari game da motsin jami’an tsaron.
An ce jami'an tsaron sun fito ne daga gidan gwamnati da ke Gusau domin aikin musamman na kare matafiyi a hanyar saboda yawaitar hare-hare a yankin.
“Jami’an sun fito daga gidan gwamnati domin taimakawa matafiya, amma kafin su wuce Gidan-Giye, sai kawai muka ji karar harbe-harbe."
"Daga nan ne muka gano cewa an kashe dukkansu nan take. Bayan haka, ‘yan bindigan sun tsere cikin daji a kan babura."
- Ya'u Musa
An kai gawarwakin jami'an da suka mutu zuwa babban asibitin tarayya da ke Gusau, inda aka tabbatar da rasuwarsu.

Source: Original
Gwamnan jihar Zamfara ya yi ta'azyya
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi ta’aziyya da alhini bisa wannan mummunan lamari.
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, gwamnan ya yi addu'ar Allah Ya jikan jami'an tsaron da aka kashe.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Na samu rahoto mara daɗi na kwanton ɓauna da 'yan bindiga suka yi wa jami'an tsaron 'yan sanda da Askarawa a hanyar Funtuwa zuwa Gusau inda suka kashe jami'ai takwas."
"Allah (T) Ya jiƙansu, Ya ba iyalai da 'yan uwansu haƙurin wannan rashi. Muna roƙon Allah (T) Ya kawo mana karshen wannan matsala ta tsaro a duk faɗin jihar Zamfara, Arewa da ma Nijeriya gabaɗaya."
- Gwamna Dauda Lawal
Wani mazaunin Gusau, Jamilu Abdullahi, ya yi alhinin kisan da 'yan bindigan suka yi wa jami'an tsaro a Zamfara.
Ya shaidawa Legit Hausa cewa batun matsalar rashin tsaro a Zamfara na matukar damun jama'a.
"Wannan lamarin bai yi dadi ba ko kadan. Mutanen ba su da kirki ko kadan. Muna rokon Allah ya kawo mana karshen wannan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita."
- Jamilu Abdullahi
Batun sulhu da 'yan bindiga a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi magana kan sulhu da 'yan bindiga.
Gwamna Radda ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da 'yan bindigan da suke kashe mutane ba.
Sai dai, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta goyi bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla tsakanin 'yan bindiga da al'ummomi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

