Musulmin Gwamna Bago Ya Jagoranci Addu'a a Coci har Ya Burge Kiristoci
- Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya ja hankalin jama’a bayan an gan shi yana addu’ar neman zaman lafiya a coci
- Gwamnan, wanda ya fara da rera wakokin bauta ya sanar da cocin cewa yana da tabbacin shiga cocin domin addu’a ba kuskure ba ne
- Jama’a da dama sun yi martani a kan wannan lamari, inda wasu ke cewa ana kokarin kawar da zargin kisan kiristoci a Najeriya ne kawai
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Niger – Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya dauki hankalin jama’a bayan an gan shi a cikin bidiyo yana rera wakokin bauta a wani coci.
Gwamnan ya ziyarci cocin Living Faith, inda ya jagoranci Kiristoci wajen yin addu’a domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Source: Twitter
A wani bidiyo da shafin Nigeria Stories ya wallafa a X, an ga Gwamna Umaru Bago yana karɓar bututun magana, inda ya fara da furta kalmar nan: “Praise the Lord,” wanda ke nufin “Yabo da Ubangiji.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Neja ya yi addu’a a coci
A wani bidiyo daban da Oyindamola ya wallafa a X, an ga Gwamna Bago yana karkada hannunsa daga gefe zuwa gefe, yayin da ya rera wakar bauta da ta fara da: “May the Spirit of the Lord come down.”
Wannan wakar na daya daga cikin shahararrun wakokin bauta da Kiristoci ke rera wa a cocinsu, musamman a ranakun Lahadi da sauran lokutan ibada.
Gwamnan ya rera wakar, wacce ke roƙon saukar ruhin Ubangijinsu tare da goyon bayan mawakan cocin.
Bayan kammala wakar, Gwamna Bago ya yi wata addu’a da ta shahara a tsakanin Kiristoci, wacce ta fara da “Our Father who art in heaven...” har zuwa karshenta, inda suka yi addu’ar samun arziki da biyan bukatu.

Kara karanta wannan
Tofa: Peter Obi ya maka sanannen lauya a kotu, yana neman diyyar Naira biliyan 1.5
Gwamnan ya ce:
“Lokacin da na shigo wannan coci, na shaida wa kaina cewa wannan al’amari ba kuskure ba ne – wannan wani wahayi ne.”
Bago: Kiristoci sun yi murna
Alamu sun nuna cewa mahalarta cocin sun yi farin ciki da yadda Gwamna Umaru Bago ya shiga cikin harkokinsu da rera wakokin coci kamar wani daga cikinsu.

Source: Facebook
Sai dai, martanin da aka samu a dandalin X ya bambanta – wasu sun yaba da hadin kan addinai, yayin da wasu ke kallon hakan a matsayin wata dabarar siyasa.
@john_uduakobong ya ce:
“Wannan shi ne irin shugabancin da Najeriya ke bukata! Gwamna Musulmi yana halartar taron Kiristoci domin yin addu’a ga zaman lafiya da hadin kai? Wannan ne hadin kan da ya kamata mu rika murna da shi, ba rarrabuwar kawuna ba.”
@excel_sammy ya rubuta:
“'Yan siyasar Najeriya da dabarunsu kamar ‘dan juma ne da ‘dan jummai.
@gpd_worldwide ya ce:
“Har yanzu ana kashe-kashe a Arewacin Najeriya. Wannan ba zai yi tasiri ba.”
@maniac8989 ya tambaya:
“Shin wannan ba sabo ba ne?”
@ifeanyi2448 ya bayyana cewa:
“Suna kokarin yin komai domin su canza labarin kisan Kiristoci, su nuna wa duniya wani abu daban dangane da halin da ake ciki.”
@betternow40471 ya rubuta:
“Eh, irin wadannan ne shugabannin da Najeriya ke bukata. Ba wadanda ke son raba kasa bisa addini ba. Mafi yawanmu muna son kasar da za zauna cikin farin ciki da banbancin addinanmu. Gwamna manomi,Mai girma Umaru Bago, ya cancanci da yabo.”
'Yan bindiga sun kai hari Neja
A baya, mun wallafa cewa ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wasu kauyuka da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Jihar Neja, inda suka kashe wani shugaban ‘yan sa‑kai.
A cewar rahotanni, hare‑haren sun faru ne da daddare a ranar Jumma’a, 3 ga watan Oktoba, 2025, a wasu kauyuka da suka hada da Dukku da Shafini da ke yankin Rijau.
A kauyen Dukku, ‘yan bindiga sun mamaye gari da 9.20 na dare, inda suka sace Alhaji Sodangi Mohammed tare da wasu mutane shida, ami'an tsaro su ka fara aikin ceto.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


