'Ku Zama cikin Shiri,' NiMet Ta Fadi Jihohi 4 da Ambaliya Za Ta Shafa Ranar Juma'a
- Hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet), ta fitar da hasashen yanayi na ranar Juma'a, 12 ga Satumba, 2025
- Akwai yiwuwar za a yi tsawa da ruwan sama mai yawa a jihohin Arewa maso Yamma, maso Gabas da kuma ta Tsakiya
- Hukumar ta yi gargadi ga mutane cewa za a iya samun ambaliyar ruwa a Legas, da wasu jihohi uku, don haka kowa ya shirya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da hasashen yanayi na ranar Juma'a, 12 ga watan Satumba, 2025.
A cewar rahoton, ana sa ran za a samu tsawa, ruwan sama, da iska mai ƙarfi a sassan ƙasar, tare da gargadi na musamman game da yiwuwar ambaliyar ruwa a jihohi huɗu.

Source: Getty Images
A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, NiMet ta shawarci mazauna yankunan da aka yi hasashen za a samu ambaliya da su kasance a shirye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hasashen ruwan sama a Arewacin Najeriya
A safiyar ranar Juma'a, ana sa ran za a yi iska mai ƙarfi da ruwan sama a jihohin Arewa da suka haɗa da Kebbi, Sokoto, Zamfara, Kaduna, Kano, Katsina, da Taraba.
Haka kuma a Arewa ta Tsakiya, za a samu hadari tare da fitowar rana, inda ake sa ran ruwan sama kaɗan zai sauka a wasu sassan jihar Neja, Kogi, da Benue.
Da yammaci zuwa dare kuwa, ana sa ran za a ci gaba da tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a sassan jihohin Bauchi, Gombe, Adamawa, Taraba, Kaduna, Kano, Zamfara, Katsina, Sokoto, da Kebbi.
NiMet ta kuma yi hasashen tsawa da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a jihohin Nasarawa, Plateau, Kwara, Kogi, Benuwe, da kuma Babban Birnin Tarayya (Abuja).

Kara karanta wannan
'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki
Hasashen ambaliya a jihohi 4 a Kudu
A safiyar ranar Juma'a, hadari zai lullube sararin samaniya tare da yiwuwar saukar ruwan sama kaɗan a sassan kudancin ƙasar.
Sai dai da yamma zuwa dare ne ake sa ran za a samu ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a yawancin sassan yankin, wanda zai iya ɗaukar lokaci mai tsawo.
Hukumar ta kuma yi gargadi kan yiwuwar afkuwar ambaliyar ruwa a jihohin Legas, Ogun, Akwa Ibom, da Cross River.
NiMet ta shawarci mazauna jihohin da ke fuskantar ambaliyar ruwan da su kasance cikin shiri, don kare kawunansu da dukiyoyinsu.

Source: Getty Images
NiMet ta ba 'yan Najeriya shawarwari
Hukumar NiMet ta kuma gargadi direbobi kan cewa za su fuskanci wahalar tuki a lokacin da suke tuki saboda ruwan sama da iska mai karfi, wanda zai iya jawo hadurra.
NiMet ta ba da shawara da a guji neman mafaka a ƙarƙashin bishiyoyi a lokacin tsawa saboda haɗarin faɗuwar rassa, tare da ƙarfafa wa kamfanonin jiragen sama da su nemi bayanan yanayi na filin jirgi daga NiMet don shirya zirga-zirgarsu.
Ruwa ya tafi da mutane a ambaliyar Zaria
A wani labarin, mun ruwaito cewa, mutane uku sun mutu yayin da aka nemi wasu biyu aka rasa sakamakon ambaliyar ruwa a Zaria, jihar Kaduna.
An gano gawar Fatima Sani Danmarke da wani dalibi Yusuf Surajo Tudun Wada, yayin da ake cigaba da neman wata yarinya ‘yar shekara uku.
Ambaliyar ruwan ta tafi da wani mazaunin unguwar Tudun Jukun da ya yi yunkurin ceto Fatima da ‘yar uwarta, kamar yadda rahoto ya nuna.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

