'Talauci Ya Yi Muni a Najeriya,' El Rufa'i Ya ce Akwai Mafita kan Matsin Tattalin Arziki
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya ce 'yan Najeriya suna ci gaba da fada wa cikin kangin talauci
- Amma a ganinsa, akwai sakaci a dalilin da ya sa lamarin ke ta'azzara, inda ya buga misali da kasahen da ke ci gaba a yanzu
- A hannu guda kuma, Nasir El-Rufa'i ya koka a kan yadda aka samu raguwar yawan masu kada kuri’a zuwa 30% a 2023
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa an samu karin talakawa a Najeriya fiye da lokacin da aka samu ‘yancin kai a 1960.
A cewarsa, wannan abin kunya ne, duba da yadda ƙasashe kamar China da India suka samu nasarar rage talauci sosai.

Kara karanta wannan
Yaron El Rufa'i: Uba ya yi raddi ga kalamai da zarge zargen tsohon Gwamnan Kaduna

Source: Facebook
Arise News ta wallafa cewa El-Rufa'i ya ce har yanzu, Najeriya ba ta da wani cikakken tsari ko taswira ta yaki da talauci a matakin ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El-Rufa'i ya magantu kan Najeriya
El-Rufai, wanda tsohon Ministan Birnin Tarayya ne ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa a garin Owerri, Jihar Imo.
Ya ce:
“Muna bukatar sahihin tsarin da zai taimaka mana mu fitar da al’umma daga kangin talauci. Idan muka fifita yaki da talauci, zamu iya yin nasara. Muna bukatar wani shiri na tattalin arziki mai ma’ana da zai kai mu ga ga ci."
Rahotanni sun ce adadin mutanen Najeriya a 1960 bai wuce miliyan 45 ba, amma a yau ya zarce miliyan 220.
An samu karuwar talauci a Najeriya
Rahoton ya kara cewa fiye da rabin 'yan Najeriya na rayuwa a cikin talauci mai tsanani, inda su ke rayuwa a kan ƙasa da $2.15 a rana.
Kididdiga daga shekarar 2024 ta nuna cewa sama da 54% na 'yan Najeriya su na fama da matsanancin talauci, wanda ya shafi kimanin mutane miliyan 129.

Source: Facebook
Rahoton ya ci gaba da cewa mafi yawan su daga yankunan karkara, inda ake fuskantar talauci har 75% a wasu lokuta.
Baya ga batun talauci, El-Rufai ya nuna damuwarsa game da raguwar yawan masu kada kuri’a a Najeriya daga 60% a 2003 zuwa 30% a 2023.
Ya jaddada cewa dole ne a samu matsaya tsakanin manyan ‘yan siyasa wajen tabbatar da sahihan zabe, tare da bukatar amfani da na’urorin zamani wajen kada kuri’a.
Uba sani ya raba gari da El-Rufa'i?
A baya, mun wallafa cewa Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana wadanda su ka tallafa masa wajen ci gaban siyasarsa.
A cewar Uba, akwai manyan mutane biyu da suka fi taka rawa a rayuwar siyasar sa, su ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma marigayi Cif Gani Fawehinmi.
Sai dai bai ambaci Nasir El-Rufa'i a matsayin daya daga cikin mutanen da su ka cicciba shi a siyasa ba, duk da tsohon gwamnan ya sa kiransa 'yarona.'
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
