Bauchi, Neja da Jihohin Najeriya 8 Sun Kinkimo wa Kansu Bashin Naira Biliyan 417
- Sababbin bayanan NBS da DMO sun nuna cewa ana bin jihohin Najeriya 31 bashin cikin gida da ya kai Naira tiriliyan 2.57
- Jihohi biyar da Abuja ne kadai suka samo masu zuba jari a zangon farko na 2025, amma sauran jihohin sun ciwo bashi ne kawai
- Rivers, Enugu, Niger su ne a kan gaba a jerin jihohi 10 da suka kinkimo bashin Naira biliyan 417 duk da karin kudi daga FACC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ana bin jihohi 31 daga cikin jihohin Najeriya 36 bashin cikin gida da ya kai Naira tiriliyan 2.57 a zangon farko na shekarar 2025.
An samu sababbin bayanai kan basussukan da ake bin jihohin ne daga rahotannin da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) da ofishin gudanar da bashi (DMO) suka fitar.

Source: Twitter
Ana bin jihohin Najeriya bashin N2.57trn
Abin da ya fi daga hankalin shi ne, jihohin sun kinkimo bashin Naira tiriliyan 2.57 ba tare da sun samu jarin kasashen waje na a zo-a-gani ba, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotannin sun kuma nuna cewa jihohi biyar ne kawai da Abuja suka samu jarin waje, inda suka samu jimillar $5.63bn, sama da $3.38bn da suka samu a farkon zangon 2024.
Duk da jarin biliyoyin daloli da suka samu, wadannan jihohi 5 da Abuja, suna ci gaba da dakon bashin cikin gida na jimillar Naira tiriliyan 1.3.
Jihohi 10 sun karbo bashin N417bn
Rahoton watanni uku-uku na ofishin DMO ya kara bayyana cewa jihohi 10 sun karbo karin bashin cikin gida da ya kai Naira biliyan 417.7 cikin shekara guda, duk da karin kudi da aka samu daga asusun tarayya (FAAC).
Jihohin da suka fi karbo karin bashi sun hada da: Rivers, Enugu, Niger, Taraba, Bauchi, Benue, Gombe, Edo, Kwara da Nasarawa.

Kara karanta wannan
Tura ta kai bango: Likitoci sun shiga yajin aiki, sun gindaya wa gwamnati sharuda
Jimillar basussukan wadannan jihohi ta karu daga Naira biliyan 884.9 a zangon farko na shekarar 2024 zuwa Naira tiriliyan 1.3 a zangon faro na 2025.
Yadda jihohin suka ci bashin N417bn
Rivers ta fi sauran jihohi da bashin Naira biliyan 364.39, sama da Naira biliyan 232.58 da ta ke da shi a zangon farko na 2024, watau karin 56.7%.
Bashin da ake bin Enugu ya yi tashin gwauron zabi a cikin shekara guda daga Naira biliyan 82.48 zuwa Naira biliyan 188.42 (karin 128.4%), inda ta karbi bashin Naira biliyan 69.14 cikin watanni uku kacal.

Source: Twitter
Taraba ta fi kowace jihar girman kason bashin da ta karba a cikin shekara guda, daga Naira biliyan 32.64 zuwa Naira biliyan 82.93 (karin 154.1%), a cewar rahoton TVC.
Bashin Niger ya karu daga Naira biliyan 86.05 zuwa Naira biliyan 143.75 (karin 67%), sai na Bauchi da ya karu daga Naira biliyan 108.35 zuwa Naira biliyan 142.40 (karin 31.4%).
Benue ta kara bashin ta daga Naira biliyan 116.75 zuwa Naira biliyan 129.82 (karin 11.2%), yayin da bashin da ake bin Gombe ya karu daga Naira biliyan 70.85 zuwa Naira biliyan 83.66 (karin 18.1%).

Kara karanta wannan
Jerin jihohin da mafi karancin albashi ya kusa N100,000 ko sama da haka a Najeriya
A hannu daya, Edo ta kara yawan bashinta daga Naira biliyan 72.39 zuwa Naira biliyan 82.40 (karin 13.8%), Kwara ta kara daga Naira biliyan 59.09 zuwa Naira biliyan 60.10 (karin 1.7%).
Hakazalika, bashin da ake bin jihar Nasarawa ya karu daga Naira biliyan 23.76 zuwa Naira biliyan 24.73 (karin 4.1%).
Gwamnatin tarayya ta daina biyan bashin jihohi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta ce ba za ta iya ci gaba da biyan basussukan da gwamnatocin jihohi suka kasa biya ba.
Babbar akawu ta kasa, ta bukaci jihohi su bullo da sababbin dabarun tara karin kudaden shiga, don rage dogaro da gwamnatin tarayya.
Dakta Sakirat Madein ta ce za a zamanantar da harkokin biyan albashi tare da bukatar ma'aikata su koyi amfani da fasahohin zamani a ayyukansu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
