DMO: Jihohi Sun Rage Karbo Bashin Gida Yayin da Kudin da Ake Bin Najeriya ya Karu

DMO: Jihohi Sun Rage Karbo Bashin Gida Yayin da Kudin da Ake Bin Najeriya ya Karu

  • Rahoton ofishin kula da basussuka a Najeriya (DMO) ya bayyana cewa jihohin kasar nan sun rage basussukan da suke karba a cikin gida da Naira Tiriliyan 1.79 cikin watanni uku
  • Alkaluman da ofishin ya fitar ya nuna cewa jihohin Arewa maso Gabas ne kan gaba wajen rage basussukan da 95%, wanda ya kai Naira Biliyan 40.69 daga Janairu zuwa Maris
  • Ragin basussukan da aka samu a jihohi na zuwa ne yayin da rancen da Najeriya ta karbo ya karu da kusan Naira Tiriliyan 24 wanda ya hada da na gwamnatin tarayya da jihohi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Ofishin kula da basussuka (DMO) ya bayyana cewa an samu raguwar basussukan cikin gida da jihohin kasar nan 35 suka karba a watanni ukun farko na 2024.

Kara karanta wannan

EFCC ta gurfanar da ma'aikacin gwamnati gaban Kotu saboda zargin hana bincike

Alkaluman da DMO ya fitar sun bayyana cewa kudin ya ragu da N1.79trn idan aka kwatanta da watannin baya da basussukan cikin gida suka kai N5.86trn a watan Disamba, 2023.

Nigeria Governors' Forum
Jihohi sun rage karbo rance a watanni ukun 2024 Hoto: Nigeria Governors' Forum
Asali: Facebook

The Cable ta wallafa cewa a bayanan da aka tattaro a watan Maris 2024, basussukan da aka karbo daga cikin gida ya kai N4.07trn wanda ke nuna samun ragin N1.79trn.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigawa ta fi sauran jihohi rage bashi

Binciken da aka gudanar ya tabbatar da jihar Jigawa ce kan gaba a jihohin kasar nan da suka rage karbo basussuka a cikin gida a farkon shekarar nan.

Rahoton ya nuna jihohin Arewa maso Yamma sun rage basussukan cikin gida da suka karbo da 95%, wanda ya kai N40.69bn.

Baya ga haka, jihohin Ondo da Kebbi sun rage bashin nasu da 77%, wanda ya kai N55.11bn da kuma 72% da ya kai 61.25bn.

Kara karanta wannan

Rahoton DMO: Bashin da ake bin Najeriya ya ƙaru da Naira tiriliyan 24 cikin wata 3 kacal

Jihohi da ragin kason bashi a gida

Jihohin kasar nan 35 ne suka yi kokari wajen rage karbo basussukan cikin gida a farko-farkon shekarar 2024; ga jerin jihohin da kason da suka rage na karbo basussuka;

1.Jigawa: -95%

2. Ondo: -77%

3. Kebbi: -72%

4. Ebonyi: -68%

4. Kogi: -68%

6. Nassarawa: -67%

7. Kaduna: -66%

8. Borno: -63%

9. Katsina: -62%

10. Taraba: -60%

11. Anambra: -54%

12. Ekiti: -48%

13. Kano: -47%

14. Kwara: -46%

14. Yobe: -46%

16. Edo: -42%

17. Zamfara: -41%

18. Osun: -40%

19. Benue: -38%

19. Niger: -38%

19. Oyo: -38%

19. Plateau: -38%

19. Sokoto: -38%

24. Bauchi: -33%

25. Bayelsa: -32%

26. Cross River: -29%

27. Adamawa: -25%

27. Akwa Ibom: -25%

27. Imo: -25%

30. Ogun: -21%

31. Gombe: -20%

32. Abia: -18%

33. Enugu: -11%

33. Lagos: -11%

35. Delta: -10%

Bashin Najeriya ya karu da N24trn

Kara karanta wannan

Tsananin zafi ya yi sanadiyyar rayuka 900, musulmai na cigiyar 'yan uwansu

A wani labarin kun ji cewa basussukan da ake bin Najeriya ya karu bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karbo rancen N6.35tn tsakanin Disambar 2023 zuwa Maris 2024.

Basussukan sun karu saboda rancen da gwamnatocin jihohin kasar nan, gwamnatin tarayya da Abuja suka karbo a cikin watannin uku na shekarar 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.