Cikin Kwana 2, Ƴan Bindiga Sun Kashe Fiye da Mutane 20 a Neja da Jihohin Arewa 4

Cikin Kwana 2, Ƴan Bindiga Sun Kashe Fiye da Mutane 20 a Neja da Jihohin Arewa 4

Akalla mutane 23 ne aka kashe a hare-haren ‘yan bindiga a Katsina, Kaduna, Kwara, da wasu jihohin Arewa uku a karshen makon nan.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rahotanni sun bayyana cewa hare-haren sun auku ne tsakanin Juma’a da Lahadi, inda kuma aka yi garkuwa da mutane da dama tare da jikkata wasu.

'Yan bindiga sun kai hare-hare jihohin Arewa 5, inda suka kashe fiye da mutane 20.
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun yana aiki a ofis dinsa da ke Abuja. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Katsina: An kashe mutane a Magajin Wando

A jihar Katsina, ‘yan bindiga sun kai farmaki garin Magajin Wando da ke karamar hukumar Dandume, inda suka kashe mutum bakwai, a cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin jihar ta tabbatar da lamarin, inda kwamishinan tsaro, Nasir Mu'azu ya ce:

“Idan ba don jami'an tsaron da gwamnatin jiha ta kafa ba, watau C-Watch, to da mutanen da suka mutu sun fi haka yawa.”

An kashe mutum 7, an jikkata 11 a Kaduna

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a Katsina, an samu asarar rayuka

Hare-hare sun ci gaba a garin Wake, gundumar Agunu, karamar hukumar Kachia, inda 'yan bindigar suka kashe akalla mutum bakwai suka mutu.

Jaridar Blueprint ta rahoto cewa 'yan bindigar sun kuma jikkata mutum 11 sannan sun yi garkuwa da mutane da dama.

Wasu mazauna kauyen, sun bayyana cewa, 'yan bindigar sun kashe mutane bakwai, sun ji wa wasu rauni, sannan sun sace wasu da dama.

Wani mazaunin garin ya ce:

"Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 'yan bindigan masu yawa sun farmaki kauyen namu, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, suka kashe mutane bakwai, suka sace wasu."

'Yan bindiga sun kashe mutane 2 a Kwara

'Yan bindiga sun kai farmaki garin Shagbe, karamar hukumar Ifelodun da tsakar dare, inda suka kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da takwas.

An ce 'yan ta'addar sun farmaki fadar Onishagbe, Sarkin Shagbe, a wani yunkuri na garkuwa da sarkin.

Sai dai, miyagun sun gamu da turjiya daga masu tsaron fada, inda aka yi musayar wuta, har aka kashe wani dan sa kai.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun cire tsoro, sun yi gaba da gaba da 'yan bindiga a jihar Sakkwato

Wani shugaban al’umma na garin ya ce 'yan bindigar sun bukaci N200m daga mazauna garin a matsayin kudin fansar mutanen da suka sace.

An kashe ma'aikata 6 a jihar Plateau

'Yan bindiga sun kashe masu hakar ma’adinai shida a wurin hakar ma’adinai da ke garin Wang, karamar hukumar Bokkos.

Yayin da Christopher Luka, wani jagora a Bokkos ya tabbatar da faruwar lamarin, wani matashi, Shanono Usman, ya ce:

“Mutanen suna aikin hakar ma’adinai ne lokacin da 'yan bindigar suka bude musu wuta.”

Daya daga cikin jami'an tsaron da ke ba da kariya a yankin, ya ce 'yan bindigar sun kashe mutum shida, yana mai cewa:

"Mun sha gargadin mutane a kan su hakura da hakar ma'adanai a yankin, amma sun ki ji. Ina da yakinin wadanda aka kashe sun je hakar ma'adanan da tsakar dare ne, bayan jami'an tsaro sun bar wajen."
'Yan bindiga sun kashe mutane 23 a Katsina, Kaduna, Neja, Filato da Kwara a karshen makon nan.
Gwamna Uba Sani ya karbi sababbin motocin da aka saya wa 'yan sandan Kaduna don kare jama'a. Hoto: @ubasanius
Source: Twitter

An kashe makiyayi, an sace manoma a Niger

'Yan bindiga sun kashe mutane yayin da suka sace manoma da matafiya masu yawa, a jerin hare-haren da suka kai garuruwan Mariga, Kontagora, Rijau da Magama a jihar Neja.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, an samu asarar rayuka

Mazauna yankunan sun ce 'yan bindigar sun fara kai hare-haren a ranar Litinin, 1 ga Satumba, har zuwa karshen mako, inda suka farmaki garuruwa da dama.

Rahoton Zagazola Makama ya nuna cewa, maharan sun yi amfani da hijabai wajen ɓatar da kamanni, kafin su sace mata da malamai a Kontagora.

Wasu daga cikin garuruwan da aka farmaka, tsakanin Litinin, 2 ga Satumba, 2025 zuwa Lahadi, 7 ga Satumba, 2025 sun hada da Atabo, Zoma, Mailema, Dusai a Mariga, Kontagora da Magama.

A harin da suka kai kauyen Dappo a gundumar Tungan Wawa, Kontogora, an kashe mutane uku, kuma sun sace mutane da dama.

'Yan bindigan Katsina sun sace mutane 130

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan bindiga sun sace mutane sama da 130 tare da kashe akalla mutum shida a hare-haren da suka kai kauyukan Katsina.

'Yan bindigan sun kai hare-haren ne a kauyuka daban-daban na karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina cikin kwanaki uku, kamar yadda rahoto ya nuna.

Harin da ya fi tayar da hankali shi ne na garin DanKurmi da ke Sabuwa, inda suka kashe mutum hudu, sannan suka yi garkuwa da akalla mutane 79.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com