'Yan Sanda Sun Dakile Shirin Masu Garkuwa da Mutane, Sun Cafke Miyagun Masu Laifi
- Jami'an rundunar ƴan sanda a Kwara, sun nuna ƙwarewa bayan samun bayanai kan mugun nufin masu garkuwa da mutane
- Ƴan sandan sun samu nasarar cafke wasu mutane da ake zargi da kitsa sace wasu mutane bayan sun yi musu barazana
- Jami'an rundunar sun gudanar da bincike inda suka cafke mutanen guda huɗu da ake zargi da yunkurin aikata laifin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kwara - Rundunar ƴan Sandan jihar Kwara ta samu nasara kan wasu miyagun masu garkuwa da mutane.
Jami'an ƴan sandan sun daƙile wani yunƙurin sace mutane har sau biyu, tare da cafke mutane huɗu da ake zargi da aikata laifin a ƙananan hukumomin Ifelodun da Baruten na jihar.

Asali: Facebook
Ƴan sanda sun cafke waɗanda ake zargi
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ya tabbatar da cafke mutanen huɗu da ake zargi, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi ta'adi, an gano gawar ɗan Majalisar da suka sace a wani yanayi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ƴan sandan ta samu nasarar a ranakun 9 da 15 ga watan Janairu, 2025, inda jami’anta suka bi sawu, suka kama mutanen huɗu da ake zargi da satar mutane.
An cafke mutanen ne a wurare daban-daban a garin Share, hedkwatar ƙaramar hukumar Ifelodun da kuma Ilesha-Baruba da ke ƙaramar hukumar Baruten.
Yadda ƴan sanda suka ceci mutanen da za a sace
Jami’an ƴan sandan sun kuma ceto mutanen da ake ƙoƙarin sacewa daga biyan kuɗin fansa na N9m da masu garkuwa da mutanen suka buƙata.
"A ranar 9 ga watan Janairu, 2025, da misalin ƙarfe 11:00 na safe, mun samu rahoto daga wasu mutane biyu daga ƙaramar hukumar Ifelodun, waɗanda aka turowa saƙonni da kiran barazana kan su biya N5m ko a sace su."
"Ta hanyar bincike na sirri, jami’an ƴan sanda sun kama wani Umar Sanni daga Tarshan Girgi, Wushishi a jihar Neja, wanda bayanan da ya bayar suka kai ga cafke Dahiru Isiaku na garin yana Share, ƙaramar hukumar Ifelodun, jihar Kwara."

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun shiga gari gari, sun kashe bayin Allah duk da gwamna ya yi sulhu da su
"Dukkansu sun amsa laifinsu, ciki har da bayar da lambobin wayar mutanen da za su yi wa barazana don amsar kuɗi daga gare su. An gurfanar da su a gaban kotu kuma an tura su gidan yari.”
"A ranar 15 ga Janairu, 2025, da misalin ƙarfe 6:30 na safe, wani mazaunin rugar Fulani da ke Ajuba, a Ilesha-Baruba, ya yi kaciɓus da wata takarda da aka ajiye a ƙofar gidansa ɗauke da lambobin waya biyu a rubuce a jiki."
"Bayan ya kira ɗaya daga cikin lambobin, wanda ya ɗauka ya yi masa barazanar cewa za su sace shi da iyalinsa idan har bai biya kudin fansa na N20m ba."
"Bayan sun yi ciniki, sun rage kuɗin zuwa N4m. Sakamakon hakan sai mutumin ya gaggauta sanar da ƴan sanda."
"Bayan gudanar da bincike tare da bin sawu, an cafke mutane biyu masu suna Tukur Muhammad da Yahaya Abdullahi."
- Toun Ejire-Adeyemi

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi garkuwa da sarki da wasu mutane 5, sun kashe mutum 1 daga ciki
Ƴan sanda sun fatattaki ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sanda sun yi artabu da miyagun ƴan bindiga a jihar Bauchi da ke yankin Arewa maso Gabas.
Jami'an ƴan sandan sun yi raga-raga da ƴan bindigan, inda suka kashe biyu daga cikinsu, tare da ƙwato makamai a hannunsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng