Najeriya Ta Mayar da Manyan 'Yan Damfaran Kasashen Waje 51 zuwa China da Tunisia

Najeriya Ta Mayar da Manyan 'Yan Damfaran Kasashen Waje 51 zuwa China da Tunisia

  • Hukumar EFCC tare da NIS sun tura wasu mutane 51 da kotu ta same su da laifin zamba ta yanar gizo ƙasashen da suka fito
  • Cikin waɗanda aka tura har da 'yan China 50 da ɗan Tunisiya guda ɗaya, wanda ya kai adadin wadanda aka mayar zuwa 102
  • EFCC ta ce cigaba da wannan mataki na nuni da cewa Najeriya ba za ta zura idanu a kan masu laifin ƙetare doka a kasarta ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) tare da haɗin gwiwar Hukumar Shige da Fice ta Najeriya sun sanar da mayar da mutane 51 zuwa ƙasashen su.

Hakan na zuwa ne bayan an same su da laifin zamba da kuma barna ta yanar gizo a cikin Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba za ta yi wa tubabbun 'yan daba auren gata a Kano

'Yan kasashe waje da Najeriya ta mayar kasashen su.
'Yan kasashe waje da Najeriya ta mayar kasashen su. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Legit ta ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na X.

Matakin ya hada da 'yan China 50 da ɗan ƙasar Tunisiya guda ɗaya, wanda ya sanya jimillar waɗanda aka tura zuwa ƙasashen su zuwa 102 tun daga ranar 15 ga watan Agusta, 2025.

EFCC ta ce mutanen na daga cikin sama da 190 da aka kama a wani samame da aka gudanar a Legas, wanda aka ce ya shafi manyan ƙungiyoyin ƙasashen waje masu zamba.

Najeriya ta kori 'yan kasashen waje

EFCC ta ce mayar da masu laifuffukan wani ɓangare ne na tsare-tsaren da ake gudanarwa domin tabbatar da cewa Najeriya ba ta zama mafakar ’yan damfara daga ƙasashen waje ba.

Hukumar ta bayyana cewa hukuncin da kotu ta yanke da kuma mayar da waɗannan mutane ƙasashen su wata hujja ce ta jajircewar gwamnati wajen kare harkokin tattali da tsaron ƙasa.

Kara karanta wannan

'Akwai matsala a N70, 000,' Amurka ta fitar da rahoto kan mafi karancin albashin Najeriya

Yadda aka yi da samamen kama su

Waɗanda aka mayar din suna cikin mutum 192 da jami’an tsaro suka cafke a Legas bayan samun sahihan bayanai kan ayyukan wata babbar ƙungiyar zamba ta yanar gizo.

An bayyana cewa ƙungiyar na da alaka da wasu gungun ’yan ƙetare da ke da hannu wajen salwantar da kuɗin kamfanoni da kuma lalata tsarin sadarwa a sassan duniya.

Karin 'yan kasashe waje da Najeriya ta mayar kasashen su
Karin 'yan kasashe waje da Najeriya ta mayar kasashen su. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Muhimmancin matakin ga Najeriya

Punch ta wallafa cewa EFCC ta jaddada cewa wannan aiki ya nuna jajircewar Najeriya wajen ganin ta kare sunanta da martabarta a idon duniya.

A ƙarshe, hukumar ta bayyana cewa akwai wasu mutane da dama da aka same su da irin wannan laifi waɗanda za a ci gaba da mayarwa ƙasashen su a kwanaki masu zuwa.

An ceto yaran da aka sace a Adamawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Adamawa ta yi nasarar ceto yaran da aka sace aka kai su Anambra.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kama makamai ana shirin tafiya da su jihar Kaduna daga Borno

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa wata mata da aka kama ake zargi da satar yaran a karamar hukumar Yola ta Arewa.

Gwamnatin Adamawa ta bayyana cewa matar na sayar da yaran a kan kudi N800,000 zuwa N1.7m a Kudancin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng