'Yan Damfara Sun Yi Kutse a Bankunan Najeriya, Sun Sace N1bn Daga Asusun Kwastomomi

'Yan Damfara Sun Yi Kutse a Bankunan Najeriya, Sun Sace N1bn Daga Asusun Kwastomomi

  • Ana ci gaba da tafka zamba da sata a bangaren bankunan Najeriya inda kwastomomi ke asarar kudadensu
  • A cikin watanni uku na farkon 2023, an yi asarar kusan Naira biliyan daya ta hanyar mazambata daban-daban
  • An yi wadannan haramtattun ayyukan ne ta amfani da ATM, katunan cire kudi, bankin tafi da gidanka, PoS, ceki da sauransu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kusan Naira Biliyan 1 ne aka yi hasararsu ta dalilin zamba da sata ta hanyoyin biyan kudi da mu'amalar yau da kullum a cikin kwata na farko na 2023.

Hakan ya biyo bayan fargabar da Hukumar Inshorar Ajiyar Kudi ta Najeriya (NDIC) ta bayyana kan yawaitar satar da ake samu a bankuna.

An bayyana hakan ne a cikin wani rahoto mai suna, "Rahotanni kan zamba da sata a bankunan Najeriya", wanda cibiyar horar da harkokin kudi (FITC) ta buga kwanan nan.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Kutsa Katafaren Rumbun Ajiyar Kayayyaki Na Ɗan Majalisa, Sun Tafka Ta'adi, An Rasa Rayuka a Arewa

Yadda aka sace kudin mutane a bankunan Najeriya
Kudaden Najeriya na daga kudade masu daraja a Afrika | Hoto: Central Bank of Nigeria
Asali: Getty Images

Kimanin Naira miliyan 472 ne aka yi asarar ta hanyar hanyoyin biyan kudi daban-daban da suka hada da yanar gizo, ATM, reshen banki, wayar hannu, da tashoshin PoS a kwata na farko na 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A hakan, an samu raguwar 12.3% daga Naira biliyan 3.6 da aka samu a kwatan karshe na 2022.

Haka kuma an yi asarar Naira biliyan 459 ta dalilin zamba ta hanyoyin hada-hadar kasuwanci da suka hada da kati, ceki da tsabar kudi.

Wannan ya nuna gagarumin raguwar 85.40% daga Naira biliyan 3.1 da aka samu a kwata na hudu; na karshen 2022.

Kudin da aka yi hasararsu ta hanyar katin cire kudi da zamba

Bayan nazarin asarar da aka samu daga ayyukan zamba daban-daban a cikin kwata na farko na 2023, wani lamari mai ban mamaki ya bayyana.

Kara karanta wannan

Hukumar FIRS Ta Tara Tiriliyan 5.5 a Watanni 6, Harajin Da Ba a Taba Samu a Tarihi Ba

Musamman, adadin da aka yi hasararsa ta hanyar damfara na katin kudi ya shaida raguwar 90.21%, inda ya ragu daga Naira biliyan 3.03 a kwata na 4 na 2022 zuwa Naira miliyan 296 a kwata na 1 na 2023.

Akasin haka, an samu karuwar 35.89 cikin dari ta hanyar damfara, inda aka samu hasarar daga Naira miliyan 120 a kwata da ta gabata zuwa Naira miliyan 163 a cikin Q1 2023.

Kudi da aka yi asararsu ta injunan ATM, yanar gizo, wayar hannu da PoS

Binciken adadin da aka rasa ta hanyoyi daban-daban na biyan kudi ya nuna abubuwa masu daukar hankali. Musamman ma, ganin an samu karuwar asara mai yawa saboda zamba a injunan ATM da cibiyoyin bankuna a Najeriya.

Asara ta hanyar ATM ta haura daga Naira miliyan 949 zuwa Naira biliyan 1.6, wanda hakan ya nuna karuwar 68.51% cikin dari.

Hakazalika, asarar da ta shafi zamba a rassan bankunan ya karu da 43.86% cikin dari, inda ya kai Naira miliyan 172.56 daga adadin da ya gabata na Naira miliyan 119.95.

Kara karanta wannan

Ingila Na Shirin Karbewa Tsohon Gwamnan Najeriya Naira Biliyan 100 a Kotu

Sabanin haka, an samu raguwa a fannin zamba ta yanar gizon da 95.38%, inda asarar ra ragu zuwa Naira miliyan 130.8 daga Naira biliyan 2.83 a kwatan karshe na 2023 da ta gabata.

Bugu da kari, a bangaren wayar hannu da POS, an samu raguwar 15.76% da 43.86%, bi da bi.

Damfara ta tsabar kudi da ta ceki sun ragu

A ko'ina a fannin nan, an samu raguwa a adadin da rahoton zamba ke kunshe dashi a bangarorin da suka shafi damfara ta tsabar kudi da kuma ceki.

Zamban tsabar kudi ya samu raguwar 7.28%, inda adadin mazambata ya ragu daga 151 zuwa 140.

Hakazalika, zamba ta katin kudi ya samu raguwar 15.12%, ya ragu daga adadi 11,566 zuwa 9,817.

Hakanan, zamba ta ceki ya samu raguwa mai yawa na 60.87%, tare da ba da rahoton samun yin zambar sau 9 kawai sabanin 29 da ya gabata a bara.

Shigar ma'aikatan banki ayyukan zamba

Kara karanta wannan

Emefiele: Lauyoyi Sun Zargi DSS Da Musu Barazana, Sun Fadi Dalili Daya Tak Da Yasa Ake Rike Da Shi

A cikin kwata na farko na 2023, wani yanayi mai ban mamaki ya bayyana yayin da shigar ma'aikatan banki cikin ayyukan zamba ya nuna karuwar 89.47%.

Adadin ma'aikatan da ke shiga lamarn ya haura daga mutane 38 zuwa 72, lamarin da ya haifar da damuwa sosai a bangaren hada-hadar kudi.

A cikin kwata na farko na 2023, bankunan sun dauki kwakkwaran mataki kan hakan ta hanyar dakatar da ma'aikata goma sha biyar (15) da ke cikin irin wadannan ayyukan.

Wannan adadi ya nuna an samu raguwar 25% cikin dari idan aka kwatanta da kwatan karshe na 2022, inda ma’aikatan banki goma sha biyu (12) suka rasa aikinsu saboda irin wadannan dalilai.

A wani bayanin da ya bambanta da wannan, an sami raguwar 8.08% na ayyukan zamba daga wadanda ba a ma’aikatan banki ba.

Adadin ya ragu daga 13,436 na ‘yan damfarar waje da aka ruwaito a cikin kwata na karshen 2023 zuwa 12,351 a cikin kwata na farkon 2023.

Kara karanta wannan

Attajiran Najeriya, Dangote, Rabiu, Adenuga Sun Rasa Sama Da N423bn Cikin Awanni 24 Kacal

Kudi sun rage a asusun kamfe, Bola Tinubu ya dawowa dam’iyyar APC da N2.4m

A wani labarin, jam’iyyar APC ta karbi wasu kudi daga kwamitin da ya yi aikin tallata takarar Tinubu-Shettima a zaben shugaban kasa a kasashen ketare.

Punch ta ce kwamitin harkokin kasar wajen yakin neman zaben APC a 2023 ya dawo da Naira miliyan 2.4 zuwa ga uwar kwamitin kamfe na PCC.

Wadannan kudi sun kasance ragowar da aka bari a akawun din karamin kwamitin da aka bari da dawainiyar yi wa takarar Bola Tinubu kamfe a ketare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel