Tabbatar da Juma’a a Matsayin Ranar Hutu da Bukatu 2 da MURIC Ta Nema

Tabbatar da Juma’a a Matsayin Ranar Hutu da Bukatu 2 da MURIC Ta Nema

  • Kungiyar MURIC ta bukaci kafa kotunan Shari’a a jihohin Kudu maso Yamma da kuma ranar Juma’a a zama hutu
  • MURIC ta ce Musulmi na fama da rashin adalci wajen aure da hutu, inda Nasara ke cin gajiyar dokokin da suka fi rinjaye
  • Majalisar Dattawa ta ce za ta yi nazari kan dukkan bukatun da aka gabatar domin daukar matakin da ya dace

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jihar Lagos - Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta tura bukata ta musamman ga hukumomi a Najeriya.

Kungiyar MURIC ta bukaci a sauya kundin tsarin mulki domin kafa kotunan Shari’a a jihohin Kudu maso Yamma baki ɗaya.

MURIC ta bukaci kafa kotunan shari'a
MURIC ta bukaci sanya Juma'a a ranar hutu. Hoto: MURIC.
Asali: Facebook

Bukatun da MURIC ta tura ga hukumomi a Najeriya

Kungiyar ta kuma bukaci a ayyana ranar Juma’a a matsayin hutu na kasa, domin ba Musulmi damar gudanar da ibadarsu cikin sauki da walwala, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ta hannun Dr. Jamiu Busari, ya gabatar da wannan bukata a wajen sauraron jama’a na Kudancin Najeriya.

MURIC ta ce babu ko kotu daya ta Shari’a a Kudu maso Yamma duk da yawan Musulmi, wanda hakan ya sabawa tarihi kafin zuwan Turawa.

Akintola ya ce ya kamata a kafa kotunan Shari’a a jihohin Kudu maso Yamma da Edo, inda Musulmi ke da yawan gaske.

Ya ce kotunan za su shafi Musulmi kawai, ba za su shafi wadanda ba Musulmi ba don tabbatar da adalci da zaman lafiya.

MURIC ta bukaci kafa kotunan Musulunci a yankin Tinubu
MURIC ta bukaci sanya Juma'a a matsayin ranar hutu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

MURIC ta bukaci daidaito tsakanin Kiristoci da Musulmi

Har ila yau, kungiyar ta nemi a daidaita adadin hutun addini na kasa, tana mai cewa yanzu hutu guda biyar na Kirista ne, uku na Musulmi.

Ta bukaci a hada da sabuwar shekarar Musulunci a matsayin hutu na kasa, tunda wasu jihohi sun riga sun amince da hakan, Punch ta ruwaito.

MURIC ta kuma koka da yadda aure na Nikkah ba ya samun karbuwa a hukumance, wanda ke cutar da Musulmi a muhimman al’amura.

A karshe, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jubrin Barau, ya ce za su duba dukkan bukatun da aka gabatar a taron domin tabbatar da adalci a tsakani.

Ya ce Majalisar za ta yi bitar bukatun kuma ta mikawa taron kasa domin yanke hukunci daidai da abin da ya dace.

Wannan ba shi ne karon farko ba da kungiyar ke yawan tura bukatu irin wannan domin ganin an samu adalci a tsakanin addinai ghuda biyu da ake da shi a Najeriya.

An zargin da shirin korar Musulmi

Kun ji cewa wasu masu shigar dodanni sun kai hari a masallaci da gidan limami a Oke Agbe, Jihar Ondo, inda suka doki matarsa da ’ya’yansa.

MURIC ta ce sarkin garin ya yi wa Musulman da aka zalunta tara, tare da barazanar korarsu daga gari idan ba su biya tarar awaki da tumaki ba.

Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta ce lamarin ya ci karo da tsarin mulki, tare da neman a hukunta masu laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.