“Za Mu Barranta da Duk Dan Siyasar da Bai Amfanarmu Ba”: MURIC Ta Gargadi ’Yan Siyasa Musulmai a Najeriya

“Za Mu Barranta da Duk Dan Siyasar da Bai Amfanarmu Ba”: MURIC Ta Gargadi ’Yan Siyasa Musulmai a Najeriya

  • MURIC a ranar Asabar, 10 ga watan Yuni, ta yi Allah wadai da Rauf Aregbesola, tsohon gwamnan jihar Osun kuma tsohon ministan harkokin cikin gida na Najeriya
  • Kungiyar ta addinin Islama ta ce Aregbesola sartsen wuya ne kuma barrantacce a cikin al’ummar Musulmin Kudu maso Yamma
  • Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya kuma yi barazanar cewa kungiyar za ta saka sunayen ‘yan siyasa Musulmi da ke nuna halaye irin na Aregbesola a bakin jadawali

Osogbo, jihar Osun Shahararriyar kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), a ranar Asabar, 10 ga watan Yuni, ta ce tana zuba ido kan ‘yan siyasa Musulmi a fadin Najeriya, musamman masu rike da mukaman gwamnati.

Kungiyar MURIC ta ce za ta saka sunayen duk wasu 'yan siyasar da ba sa amfanar Musulmi a cikin bakin jadawali, musamman idan suka dabi'antu da halayen tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, inji rahoton The Sun Nigeria.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: DSS Ta Yi Martani Kan Zargin Kama Gwamnan CBN

MURIC za ta barranta dan 'yan siyasar da basa amfanar Musulmai
Shugaban kungiyar MURIC, Ishaq Akintola | Hoto: Sahara Reporters
Asali: Facebook

Muna zuba muku ido: MURIC ta gargardi 'yan siyasa Musulmi a Najeriya

Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan bayan da tsohon ministan kuma tsohon gwamnan ya nemi afuwa kwanaki biyu da suka gabata amma daga baya aka ce ya musanta neman afuwar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar ta Islama wadda ta bayyana afuwar Aregbesola a matsayin "maras ma'ana" ta yi amfani da damar wajen gargadin 'yan siyasa Musulmi a kasar, kamar yadda jaridar Eagle Online ta ruwaito.

A wani bangare sanarwar da MURIC ta fitar, ta ce:

“Muna kallon ‘yan siyasa Musulmi a duk fadin Najeriya musamman masu rike da mukaman gwamnati a cikinsu.
"Za mu sanya sunan duk wani daga cikinsu da ya tabbata cewa ba shi da wani amfani ga Musulmin da ke kusa da shi da kuma wadanda suka yi koyi da bakar tinkiya."

Kara karanta wannan

Da Dumi Dumi: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Gwamnan CBN, Emefiele

MURIC ta nemi a Kirista shugabancin majalisa ta 10

A wani labarin, kungiyar Kare Hakkin Musulmai (MURIC) ta bukaci dukkan Musulmai masu neman takarar shugabancin majalisar dattawa ta 10 da su janyewa Kirista kuma dan Kudu.

Kungiyar ta ce tana goyon bayan bai wa Kirista dan Kudu mukamin ne don samun daidaito a kasar baki daya.

Babban Daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya fidar da wannan sanarwa a ranar Laraba 17 ga watan Mayu, jaridar Daily Trust ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel