Rashin Daraja: An Kama Babban Limamin Masallaci da Aukawa Ƙaramar Yarinya
- Rundunar ‘yan sandan Osun ta kama wani malamin addini da ake zargi da lalata wata yarinya ‘yar shekara takwas a Ede
- Lamarin ya faru a unguwar Babasanya-Araka inda jama’a suka taru suka kai hari kan wanda ake zargin kafin a mika shi ga Amotekun
- Kwamishinan Amotekun da wasu mazauna sun tabbatar da cewa wanda ake zargin limami ne kuma yana koyar da Alkur’ani a unguwar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Osun - Rundunar ‘yan sandan jihar Osun a ranar Asabar ta tabbatar da kama wani malamin Musulunci kan zargin lalata.
Ana zargin mutumin mai suna Kadiri da da lalata da yarinya bayan mahaifiyarta ta aike ta shago sayan kaya.

Asali: Original
An kama limami da zargin lalata da yarinya
Lamarin ya faru ne a Babasanya-Araka, Ede, wanda ya jawo tarzoma daga jama’a da suka kama wanda ake zargin suka kai masa hari, Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun ‘yan sanda, Abiodun Ojelabi, ya ce an tura jami’ai wurin da lamarin ya faru bayan an kai rahoto.
Ya ce:
“An kawo rahoton, sai muka tura jami’ai zuwa wurin. Lokacin da suka isa, sojojin Amotekun suka damke shi suka mika mana.
“Yanzu yana hannunmu. Amma muna so ofishin Divisional ya fara bincike kafin a mika shi zuwa SCID."
Kakakin Amotekun, Idowu Yusuf, ya kara bayani inda ya ce wanda ake zargin limami ne a wani masallaci a unguwar.
Ya tabbatar da cewa mutumin yana da makarantar Islamiyya wanda ya ke amfani da ita domin koyar da dalibai.
Ya kafa da cewa:
“Yana kuma da makarantar Islamiyya a yankin inda yake koyar da dalibai, yan sanda za su ci gaba da bincike.”

Asali: Twitter
Mazauna yankin sun fadi yadda aka yi
Wani mazaunin unguwar Babasanya-Araka, da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana yadda lamarin ya bayyana, cewar The Nation.
“Yarinya ‘yar shekara takwas ta bace na wasu sa’o’i ranar Asabar, mahaifiyarta ta fara nemanta ko’ina.
“Bayan an gano ta, tana kuka kuma tana zubar da jini."
- Cewar mazaunin yankin
Turjiya da matasa suka yi na kubutar da dattijon
Rahotanni sun tabbatar da cewa na dauki yarinyar zuwa asibiti a garin Ede domin duba lafiyarta kamar yadda aka saba.
Wasu majiyoyi suka ce an so a gudu da dattijon da ake zargin domin tsaratar da rayuwarsa amma matasa suka ki amincewa.
An ce matasan sun yi kokarin dakile neman tseratar da malamin domin tabbatar da cewa ya fuskanci hukunci daidai abin da ya aikata a yankin.
An tura malami kurkuku kan zargin lalata
Mun ba ku labarin cewa kotu ta yanke hukuncin ɗaurin rai da rai kan wani Malamin Musulunci, Alani Rafiu bayan kama shi da laifin kwanciya da ƙaramar yarinya.
An kama malamin ne bisa lalata rayuwar yarinya ƴar shekara 14 a cikin masallaci a yankin Ikotun a jihar Lagos.
Mai shari'a Rahman Oshodi ya ce wanda ake zargin ya ci amanar da aka ba shi na kula da yarinyar da ba ta ilimi a matsayinsa na Malami.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng