Jigawa: Dattijo Mai Shekaru 70 Ya Hallaka Ƙanwarsa kan Kayan Gado

Jigawa: Dattijo Mai Shekaru 70 Ya Hallaka Ƙanwarsa kan Kayan Gado

  • Wani magidanci dan shekara 70, Adamu Yakubu, ya kashe 'yar uwarsa Hannatu Hashimu a Galadanchi, karamar hukumar Dutse a jihar Jigawa
  • Rundunar ‘yan sanda ta ce rikici ya fara ne saboda rabon gado, inda rikicin ya rikide ya zama fada har aka kashe matar
  • An garzaya da ita asibiti bayan ta fadi, amma likita ya tabbatar da rasuwarta yayin da aka kama wanda ake zargi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dutse, Jigawa - Wani lamari mai tayar da hankali ya auku a kauyen Galadanchi, karamar hukumar Dutse a jihar Jigawa.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa wani dattijo mai shekaru 70 ya hallaka kanwarsa kan filin gado a jihar.

An cafke dattijo kan kisan kai a Jigawa
Yan sanda sun kama dattijo kan kisan kai a Jigawa. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yan sanda sun tabbatar da kama dattijon a Jigawa

Hakan na cikin sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Shi’isu Adam ya fitar a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adam ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ranar 1 ga Yuli, 2025 da misalin karfe 3:30 na rana.

Rundunar ta ce tana bincike kan zargin kisan kan da ya faru a kauyen Galadanchi da ke karamar hukumar Dutse.

Ya ce:

“Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa tana binciken wani lamari na kisan kai da ya faru a Galadanchi, karamar hukumar Dutse, ranar 1 ga Yuli.
“Wanda ake zargi, Adamu Yakubu mai shekara 70, ya kashe ‘yar uwarsa Hannatu Hashimu mai shekara 45, saboda rikici kan rabon filin gado."

SP Adam ya kara da cewa rikicin ya fara ne da gardama da baki, amma ya rikide zuwa fada, inda ya buge ta da sanda har ta mutu.

Ana zargin dattijo da kisan kanwarsa a Jigawa
An kama dattijo da ya kashe kanwarsa a Jigawa. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

Jigawa: Yadda marigayiyar ta mutu a gidanta

Marigayiyar ta bar gidan cikin fushi, amma tana shiga gidan mijinta ta fadi, lamarin da ya sa aka garzaya da ita asibitin Dutse.

Sai dai likitan da ke bakin aiki a asibitin ya tabbatar da rasuwarta, wanda hakan ya jefa iyalanta cikin kunci da jimami.

Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa an kama dattijon da ake zargi, yana hannunsu yanzu yana taimakawa da bincike da ake gudanarwa.

Abin da yan sanda suka ce ga iyalanta

Haka kuma SP Adam ya ce sanda da aka yi amfani da ita wajen dukan marigayiyar an same ta, kuma an ajiye ta a matsayin shaida.

Rundunar ‘yan sandan ta nuna bakin ciki kan lamarin, ta kuma bukaci jama’a su rika warware matsaloli ta hanyar lumana da bin doka.

A karshe, rundunar ta mika ta’aziyyarta ga iyalan marigayiyar, tare da tabbatar da cewa za a tabbatar da hukunci kan lamarin.

Yan sanda sun ragargaji miyagu a Jigawa

Mun ba ku labarin cewa rundunar ƴan sandan Najeriya ta samu nasarar hallaka wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

A wani samame na daban da aka kai a jihar Jigawa, ƴan sanda sun ceto wata dattijuwa ƴar shekara 80 mai suna Hajiya Hajara, wadda aka sace daga ƙauyen Sarbi, a jihar Kano.

Hakazalika ƴan sanda sun kuma ceto wasu wadanda aka yi garkuwa da su a birnin tarayyar Nigeria, Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.