Rigiji Gabji: Dan Najeriya Ya Sace Miliyoyin Bikin Rantsar da Donald Trump

Rigiji Gabji: Dan Najeriya Ya Sace Miliyoyin Bikin Rantsar da Donald Trump

  • FBI ta kama wani matashi Ehiremen Aigbokhan daga Legas da zargin damfarar ₦460m ta hanyar Kirifto
  • Aigbokhan ya yi amfani da adireshin imel na bogi don karɓar kuɗin da aka ware wa bikin rantsar da Donald Trump
  • Bayanan kotu sun nuna cewa an tura kuɗin ne zuwa wasu asusun kudin Kirifto da ke da alaƙa da Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America – Hukumar bincike ta FBI a Amurka ta bayyana cewa tana neman mallakar kadarorin wani matashi daga jihar Legas mai suna Ehiremen Aigbokhan.

Hakan na zuwa ne bayan da aka zarge shi da damfarar kuɗin da suka kai sama da Naira miliyan 460, da aka tanada domin bikin rantsar da Donald Trump a shekarar 2025.

Shugaban Amurka, Donald Trump a wani taro.
Shugaban Amurka, Donald Trump a wani taro. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jaridar Independent ta ce takardun kotun Amurka sun nuna cewa Aigbokhan da abokansa sun kirkiri adireshin imel na bogi na shugabannin kwamitin rantsar da Trump.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan kirkirar imel din ne suka yaudari wani mai bayar da tallafi ya tura musu kuɗin Kirifto ba tare da ya sani ba.

Yadda aka sace kudin rantsar da Trump

A ranar 26 ga Disamba, 2024, dan damfarar ya samu nasarar karɓar $250,300 daga hannun mai tallafin, wanda ya kai darajar fiye da Naira miliyan 460 a lokacin.

Rahoton CNBC ya nuna cewa bayan samun kudin, ‘yan damfarar sun watsa su cikin asusu daban-daban, inda aka raba kimanin $215,000 cikin ƴan kwanaki.

Hukumar FBI tare da haɗin gwiwar kamfanin Tether na Kirifto, sun gano zambar da 'yan damfarar suka yi, inda suka rufe asusun nan take a ranar 31 ga Disamba, 2024.

Yadda Amurka ta gano dan Najeriyan

Bayan bincike mai zurfi, FBI ta gano cewa Ehiremen Aigbokhan yana Legas, kuma an danganta shi da wasu asusun Kirifto da ke da alaƙa da sunansa a manhajar Binance da ke Najeriya.

Bayanan kotu sun ce Aigbokhan yana da hannu wajen wasu ayyukan zamba da kuma satar kuɗi ta hanyar Kirifto a faɗin duniya.

Dabarar da damfarar Najeriya ya yi

Rahotanni sun ce Aigbokhan ya yi amfani da adireshin imel mai kama da na Steve Witkoff, wanda shi ne shugaban kwamitin rantsar da Trump, domin yaudara.

Wannan zamba ta sa an karkatar da kuɗin zuwa wajen da ba a nufa ba, lamarin da ke da wahalar ganowa da dawo da kuɗin saboda tsari mai rikitarwa na fasahar Kirifto.

FBI na bincike kan yadda aka sace kudin rantsar da Trump
FBI na bincike kan yadda aka sace kudin rantsar da Trump. Hoto: Getty Images
Asali: UGC

Lauyar gwamnatin Amurka, Jeanine Pirro, ta gargadi masu tura kuɗin Kirifto da su rika taka tsantsan kafin tura kudi.

Trump ya ki gayyatar Najeriya taro Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa Atiku Abubakar ya yi magana kan yadda shugaban Amurka Donald Trump ya ki gayyatar Najeriya taron harkokin kasuwanci.

Atiku Abubakar ya ce gazawar shugaba Bola Ahmed Tinubu ce ta jawo Donald Trump bai gayyaci Najeriya ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa Najeriya ta samu koma baya a karkashin Tinubu, musamman a harkokin diflomasiyya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng