Fulani Sun Bijirewa Gwamnan Bauchi, Sun Ki Yarda da Kirkirar Sababbin Masarautu

Fulani Sun Bijirewa Gwamnan Bauchi, Sun Ki Yarda da Kirkirar Sababbin Masarautu

  • Al'umar Fulani a jihar Bauchi sun ƙi amincewa da yunkurin Gwamna Bala Mohammed na ƙirƙirar sababbin masarautu a jihar Bauchi
  • Kungiyar Fulani ta Daddo Pulaku ta ce za su ci gaba da biyayya ga masarautu shida da ake da su a Bauchi, don zaman lafiya da haɗin kai
  • Daddo Pulaku ta gargadi gwamnatin Bauchi kan cewa kirkirar sababbin masarautu zai iya kawo ƙabilanci da kuma haifar da tashin hankali

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Al'ummar Fulani a jihar Bauchi, ƙarƙashin kungiyar Daddo Pulaku sun nuna adawa ga shirin ƙirƙirar sababbin masarautu da gwamnatin jihar ta gabatar.

Daddo Pulaku ta bayyana cewa babu wata ƙungiyar Fulani ko wani bafullatani da ya kamata a tilasta masa karbar sabon tsarin sarauta ba tare da amincewarsa ba.

Fulani sun bijirewa gwamnan Bauchi kan shirinsa na kirkirar sababbin masarautu a jihar
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed Abdulkadir. Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Matsayin Fulani kan kirkirar masarautu a Bauchi

Mai magana da yawun kungiyar Daddo Pulaku, Aminu Tukur ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai a a ranar Alhamis a Bauchi, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aminu Tukur, ya ce wannan matsaya ta fito ne daga dattawa, malamai, masu rike da sarautun gargajiya, matasa, ƙwararru da shugabannin Fulani daga ƙananan hukumomi 20 na jihar.

Ya ce kungiyar ta dauki wannan matsaya bayan doguwar tattaunawa, wacce take nuna alamar zaman lafiya, haɗin kai, da kuma bin ƙa'idodin tsarin mulki na kasa.

'Muna biyayya ga masarautu 6" - Fulani

Shugaban kungiyar ya bayyana cewa:

“Muna sake tabbatar da girmamawa da biyayyarmu ga masarautun da ake da su jihar Bauchi."
“Masarautu shida da muke da su: Bauchi, Katagum, Misau, Ningi, Jama’are da Dass, su ne ginshiƙan tarihin al’adu da ɗorewar haɗin kai a jihar.
“Waɗannan masarautu sun taka muhimmiyar rawa wajen daidaita zamantakewa da wanzar da zaman lafiya tsakanin ƙabilu da addinai daban-daban.

"Al'ummar Fulani sun kasance wani ɓangare ne na waɗannan cibiyoyin tun lokacin da aka kafa su, suna ba da gudummawa ga ci gaban su ta hanyar biyayya, shugabanci, da kuma kula da su."
Fulani a Bauchi sun fadawa gwamnan jihar cewa za su bi masarautu 6 da ake da su, ba wai sababbi ba
Wani bafullatani yana kiwo a wani yanki na Arewacin Najeriya. Audu Marte
Asali: Getty Images

An gargadi gwamna kan kirkirar masarautu

Yayin da ta amince da ‘yancin kowace al’umma na neman wakilci da riko da sarautun gargajiya, ƙungiyar ta yi gargaɗi cewa shirin ƙirƙirar masarautun zai zama tamkar kawo ƙabilanci a tsakanin 'yan jihar.

"A matsayinmu na 'yan ƙasa masu bin doka da son zaman lafiya da ci gaban jihar Bauchi, za mu bayyana a fili cewa Fulanin jihar Bauchi ba sa son a kakaba musu wata sabuwar masarauta, muna so a tsaya a kan masarautu shida da ke akwai yanzu.
“Muna nan daram a kan biyayyarmu ga masarautun tarihi da muka daɗe muna rayuwa a ƙarƙashinsu cikin mutunci da zaman lafiya.
"Tilasta mana shiga sababbin masarautu da aka ƙirƙira ba tare da yardarmu ba zai raunana haɗin kai, zai kawo cikas ga daɗaɗɗiyar dangantakar al'umma, kuma zai iya haifar da tashin hankali da sauran rigingimu."

- Aminu Tukur.

Gwamnan Bauchi zai gyara gidajen sarauta

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Bauchi na ci gaba da gyara fadojin sarakuna, hakimai da masu gundumomi domin ƙarfafa martabar masarautun gargajiya a jihar.

A wani mataki na baya-bayan nan, Gwamna Bala Mohammed ya bayar da umarnin gyaran fadojin masu gunduma 11 a karamar hukumar Dass.

A cewar Muslim Dabo, ɗan asalin Dass, waɗannan masu gunduma suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya, don haka sun cancanci wannan kulawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.