An Shiga Firgici a Gombe: Mutane 4 Sun Mutu, Gidaje 171 Sun Rushe Sakamakon Ambaliya
- Mummunar ambaliya ta lalata gidaje 171 a Gombe, ta kuma yi sanadiyar mutuwar mutane huɗu, wadanda galibi ƙananan yara ne
- SEMA ta bukaci mazauna jihar su daina zubar da shara a magudanan ruwa, su kuma riƙa gyara muhallinsu don kaucewa ambaliya
- Hukumar SEMA za ta kai tallafin abinci ga waɗanda abin ya shafa, kuma ta shawarci iyaye su kula da 'ya'yansu yayin da ake ruwan sama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gombe - Mummunar ambaliyar ruwa, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe watanni biyu ana tafkawa, ya jawo lalacewar gidaje 171 a Gombe.
Hukumar ba da agajin gaggauta ta jihar Gombe (SEMA) ta ce akalla gidaje 171 suka lalace sakamakon marka-markar ruwan da aka yi da ya jawo ambaliya.

Asali: Getty Images
Gidaje sun lalace, mutane sun mutu a Gombe
Haruna Abdullahi, shugaban hukumar SEMA ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da kamfanin dillacin labarai na kasa (NAN) a Gombe, ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabna SEMA ya ce sama da gidaje 15 daga kananan hukumomin Dukku, Kwami, Gombe da Akko ne suka gamu da ambaliyar ruwan.
Haruna Abdullahi ya ce illar ambaliyar ruwan ba wai ta tsaya a kan lalata gidaje ba, har ma da yawo asarar rayukan mutum hudu, wadanda mafi akasarinsu yara ne.
"Ya zuwa yanzu, mun tattabatar da lalacewar gidaje 87 a Dukku, 27 a Kwami, 30 a Gombe da kuma 27 a Akko, wanda ya hada har da wata coci.
"Wannan ne ya sanya kullum muke ta yin kiraye-kiraye ga mazauna garuruwan jihar da su kula da gyaran muhalli, musamman kwashe magudanun ruwa.
- Haruna Abdullahi.
SEMA za ta kai tallafin abinci bayan ambaliya
Domin magance wannan matsalar, shugaban na hukumar SEMA ya ce:
"Akwai bukatar mutane su kaucewa dabi'ar zubar da shara barkatai a cikin gari ko a magudanan ruwa, ya kamata su rika zubar da sharar a inda gwamnatin jihar ta tanada."
Haruna ya bayyana cewa SEMA na shirin kai tallafin abinci da kayan masarufi ga wadanda ambaliyar ta shafa, yayin da ya shawarci iyaye su sa ido kan 'ya'yansu yayin da ake ruwa.
Ya bayyana cewa tun da kananan yara ne aka fi samun rahoton ruwa ya tafi da su, to akwai bukatar iyaye su mayar da hankali sosai wajen kula da 'ya'yansu.

Asali: Getty Images
An gargadi Gombawa kan sare bishiyoyi
Ya kuma koka kan yadda ake samun kwararar hamada sakamakon sare bishiyoyi da ake yi da nufin yin gawaki ko iccen girki a wasu sassan jihar.
Haruna ya shawarci mazauna Gombe da su daina sare bishiyoyi, yana mai cewa bishiyoyin da aka dasa a kusa da gidaje na taimaka wajen rage karfin iska da tasirinta ga gidaje.
Ya kuma bukaci mazauna jihar da su yi amfani da wannan lokaci na damuna domin dasa bishiyoyi masu yawa a cikin garuruwansu, wanda zai taimaka wajen hana kwararar hamada.
Ambaliyar ruwa ta yi barna a jihohi 31 a 2025
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito SBM Intelligence ta fitar da rahoton cewa sauyin yanayi da matsalar tsaro na ci gaba da hana manoma gudanar da aikin gona a Najeriya.
A cikin rahoton, SBM ta bayyana cewa ambaliyar ruwa ta lalata hekta 180,000 na gonaki a jihohi 31, lamarin da ya shafi rayuwar mutane miliyan 1.2 a ƙasar.
Binciken ya kuma nuna cewa kimanin mutane miliyan 2.2 sun rasa matsugunansu, yayin da farashin abinci ke ci gaba da ƙaruwa sakamakon illar ambaliya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng