Sauyin Yanayi: Tsofaffin Ma’aikata da Matasa 10,000 Za Su Samu Aiki da Gwamnatin Tarayya

Sauyin Yanayi: Tsofaffin Ma’aikata da Matasa 10,000 Za Su Samu Aiki da Gwamnatin Tarayya

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa akalla tsofaffin ma'aikata da matasa 10,000 ne za su samu aiki karkashi shirin dashen itatuwa miliyan shida
  • Karamin ministan muhalli, Dr Iziaq Salako ne ya bayyana hakan yana mai cewa shirin na da nufin dakile gurbacewar muhalli
  • Ministan, ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su goyi bayan shirin ta hanyar dasa itatuwa a gidajensu da garuruwansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin daukar matasa da ‘yan fansho akalla 10,000 aikin dashen itatuwa miliyan shida a fadin kasar nan domin dakile illolin sauyin yanayi.

Gwamnatin Nijeriya ta yi magana kan dasa itatuwa miliyan 6
Minista ya ce matasan da tsofaffin ma'aikata za su dasa itatuwa miliyan 6. Hoto: @SalakoIziaq
Asali: Twitter

Gwamnati za ta ba matasa aiki

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan da aka tsige ya mayar da martani mai zafi, ya tona wani babban sirri

Karamin ministan muhalli, Dr Iziaq Salako ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da PUNCH Healthwise.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa shirin na da nufin samar da ayyukan yi ga matasan da kuma kara tattalin arzikin wadanda suka yi ritaya, tare da magance matsalar gurbacewar muhalli.

Alausa ya ci gaba da cewa, za a gudanar da shirin dashen itatuwan ne a mataki-mataki, tare da mayar da hankali kan wuraren da sare itatuwa da kwararowar hamada suka yi wa illa.

"Illolin sauyin yanayi ga al'uma" - WHO

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, sauyin yanayi na yin tasiri ga rayuwa da lafiyar bil'adama ta hanyoyi daban-daban.

WHO ta lura cewa sauyin yanayi na barazana ga kiwon lafiya, iska mai tsafta, tsaftataccen ruwan sha, wadataccen abinci mai gina jiki, da kuma muhallin zaman al'uma.

Hukumar lafiya ta duniya ta yi hasashen cewa tsakanin shekarar 2030 zuwa 2050, ana sa ran sauyin yanayi zai haifar da mutuwar mutane kusan 250,000 a kowace shekara.

Kara karanta wannan

"Ka mayar da Pam matsayin shugaban NCPC": Dattawan Arewa sun buƙaci Tinubu

Tasirin dasa bishiyoyi a Nijeriya - Gwamnati

Ministan ya ce gwamnati na shirin dasa akalla itatuwa miliyan shida domin samar da iska mai tsafta, rage zaizayar kasa, ambaliyar ruwa, da kuma kara kwarin ita kanta kasar.

Salako ya bayyana cewa shirin zai kunshi itatuwa daban-daban da suka hada da na gida da na waje wadanda suka dace da yankuna daban-daban na Najeriya.

Ministan, ya yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su goyi bayan shirin ta hanyar dasa itatuwa a gidajensu da garuruwansu.

Majalisa ta fusata kan dashen bishiyoyi

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa majalisar wakilai ta fusata kan yadda aka kashe Naira biliyan 81 wajen dashen bishiyoyi a Arewacin Nijeriya.

Kwamitin majalisar na asusun raya muhalli ne ya gabatar da korafin badakalar da ya ce an tafka a aiwatar da shirin wanda Great Green Wall Project ya dauki nauyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel