Gwamnatin Najeriya za Ta Yi Taro domin Daidaita Farashin Man Fetur

Gwamnatin Najeriya za Ta Yi Taro domin Daidaita Farashin Man Fetur

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun 23 da 24 ga Yuli, 2025 a matsayin lokutan taron kasa na masana harkar man fetur
  • Ana sa ran taron zai mayar da hankali kan tsarin farashi, wadatar albarkatu da daidaita kasuwar da aka cire tallafi daga gareta
  • Masu sayar da man fetur sun bukaci gaskiya da adalci, suna korafi kan yadda farashin fetur ke sauyawa ba tare da sanarwa ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta gudanar da taron kasa a ranar 23 da 24 ga watan Yuli domin tattauna batutuwan da suka shafi farashin man fetur.

Baya ga tattauna farashin man fetur, taron zai mayar da hankali tsarin wadatar mai a fadin Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta amince da taron farashin mai.
Gwamnatin Najeriya ta amince da taron farashin mai. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa hukumar kula da harkokin man fetur ta NMDPRA ce za ta jagoranci gudanar da taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana sa ran cewa taron zai tara manyan ‘yan kasuwa, masu tace danyen mai, wakilan gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki don tattauna hanyoyin da za a bi wajen daidaita kasuwar mai.

Za a tattauna matsalolin sauyin farashin mai

Daraktan a hukumar NMDPRA, Francis Ogaree ne ya tabbatar da ranar taron a makon da ya gabata yayin taron makon makamashi na Najeriya karo na 24 da aka gudanar a Abuja.

Ogaree ya ce tattaunawa da hadin kai na da matukar muhimmanci wajen samar da sahihin tsarin farashi a wannan zamani da aka cire tallafin fetur.

Ya ce akwai buƙatar kafa ingantaccen tsarin da zai dakile matsalolin da ke fuskantar masu sayar da mai.

Mutane na sayen fetur a gidan mai a Najeriya
Mutane na sayen fetur a gidan mai a Najeriya. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Matsalar da masu sayar da mai ke fuskanta

Shugaban kungiyar masu gidajen sayar da man fetur ta Najeriya, Billy Gillis-Harry ya ce akwai bukatar kafa tsarin da zai daidaita farashin mai a kasar.

Ya koka da yadda sauyin farashin da Dangote ke yi ba tare da sanarwa ba ke jefa 'yan kasuwa cikin asara.

Kungiyar ma’aikatan manyan kamfanonin man fetur ta kasa ta soki yadda masu kasuwancin mai ke kara farashi fiye da kima, inda suka ce bai kamata fetur ya wuce N700 zuwa N750 ba.

NMDPRA ta ce tana ɗaukar mataki

Ogaree ya ce hukumar NMDPRA ta fahimci matsalolin da ke fuskantar ‘yan kasuwa, kuma ta fara ɗaukar matakai na daidaita farashin fetur tare da karfafa jarin tace danyen mai a cikin gida.

Ya ce:

“Za mu shirya taron kwana biyu daga 23 zuwa 24 ga Yuli domin magance matsalolin mai da kuma kafa matakan samar da tsayayyen farashi.
"Kowa ya san farashin fetur batu ne mai hadari da ke buƙatar kulawa, kuma muna aiki a kai.”

Dangote zai fara raba man fetur kyauta

A wani rahoton, kun ji cewa matatar Dangote ta fitar da tsarin fara raba man fetur kyauta ga abokan huldarta.

Rahotanni sun bayyana cewa Alhaji Aliko Dangote zai tabbatar da hakan ne bayan sayen tankokin jigilar mai 4,000.

Dangote ya bukaci dukkan 'yan kasuwa masu bukatar shiga tsarin da su yi rajista da matatar shi domin cin gajiyar shirin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng