Dantata: Hukuncin kai Gawa Gari Mai Tsarki kamar Madina a Musulunci

Dantata: Hukuncin kai Gawa Gari Mai Tsarki kamar Madina a Musulunci

  • Daukar gawar marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata da ya rasu a Abu Dhabi na Dubai zuwa birnin Madina ya haifar da ce-ce-ku-ce
  • Wani malami ya ce malaman fikihu sun tattauna batun ɗaukar gawa daga gari zuwa gari domin a birne mamaci a waje mai falala
  • Malamin ya ce Malikiyya da Hanabila sun amince da hakan matuƙar ba za a samu matsala ga gawar ba kuma akwai manufa mai kyau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Masana addini sun yi bayani bayan da aka ɗauki gawar fitaccen ɗan kasuwa, marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata daga Dubai zuwa Madina domin masa jana’iza.

Wani malamin addinin Musulunci a jihar Bauchi ya bayani kan hukuncin daukar gawa daga gari zuwa wani gari mai daraja.

Malamin da ya yi bayani kan hukuncin birne gawa a wani gari. Hoto: Aliyu Muh'd Sani|Barau I Jibrin
Dantata: Hukuncin kai gawa daga wani gari zuwa kasa mai tsarki kamar Madina a Musulunci
Asali: Facebook

Sheikh Aliyu Muhammad Sani ne ya wallafa bayanin a shafinsa na Facebook kan wannan batun, inda ya ce lamarin yana da tushe a cikin Malaman mazhabobi huɗu na fiqhu da kuma hadisai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanin mazhabobi kan birne gawa a wani gari

Sheikh Aliyu ya bayyana cewa Malaman Malikiyya da Hanabila sun halasta ɗaukar gawa daga wani gari zuwa wani matuƙar ba za a cutar da gawar ba kuma akwai dalili mai kyau.

A cewarsa, dalilai masu kyau sun haɗa da neman a birne mutum a maƙabartar ‘yan uwansa, ko wuri mai albarka kamar Makka ko Madina, ko wajen da salihan bayi da shahidai.

Ya ƙara da cewa mazhabar Hanafiyya ta ƙayyade tafiyar da tazarar da ba ta wuce mil biyu ba, yayin da Shafi’iyya ta rarrabu – wasu sun haramta, wasu kuma suka karhanta lamarin.

Karin bayani kan birne mutum a gari mai tsarki

A cewar malamin, babban malamin Hanbaliyya, Ibnu Qudama, ya bayyana cewa ya halasta a ɗauki gawa zuwa wani gari idan akwai dalili mai kyau da ke da nasaba da addini ko daraja.

Ya ce:

“Ba za a ɗauki mamaci daga garinsu zuwa wani gari a birne shi ba, sai dai bisa manufa mai kyau… amma idan akwai wata manufa mai kyau, to ya halasta.”

Sheikh Aliyu Muhammad Sani ya ce Imamul Bukhari ma ya kawo hujja a littafinsa, inda ya ambato hadisin mutuwar Annabi Musa (AS), wanda ya roƙi a kai shi birnin Qudus.

Malamin ya ce malamai sun dauki bukatar birne annabi Musa a Qudus a matsayin hujja kan lamarin.

Lokacin da aka dauki gawar Dantata zuwa Baki'a a Madina.
Lokacin da aka dauki gawar Dantata zuwa Baki'a a Madina. Hoto: Barau I Jibrin
Asali: Twitter

Hukuncin birne mutum a kasa mai albarka

Sheikh Aliyu ya jaddada cewa mustahabbi ne mutum ya buƙaci a birne shi a wuri mai albarka kamar Makka da Madina.

Ya ƙara da cewa Ibn Qudama ya ce:

“An so mutum ya nemi a birne shi a maƙabartar da salihan bayi ko shahidai suke da yawa.”

Dalilin da yasa mutane ke son a birne su a Madina

Birnin Madina, wuri ne mai tsarki ga al’ummar Musulmi, wanda ke da tarihin addini mai zurfi tun zamanin rayuwar Annabi Muhammadu (SAW).

A Madina ne Annabi (SAW) ya rayu tsawon shekara goma bayan hijira daga Makka, kuma a nan ne aka birne shi a masallacinsa. Wannan ne ya sa birnin ya zama ɗaya daga cikin wuraren da Musulmi ke darajawa matuka.

Daya daga cikin abubuwan da ke sa mutane su so a birne su a Madina shi ne maƙabartar Jannatul Baqi’, inda aka binne sahabbai da dama na Annabi (SAW), ciki har da ‘yan gidansa da wasu shahararrun musulmai.

Malamai da dama sun bayyana cewa birne mamaci a wuri mai albarka yana daga cikin abubuwan da ake sha'awa.

Mazhabar Hanbaliyya da Malikiyya sun amince da kai gawa zuwa Madina matukar ba za a cutar da ita ba kuma akwai dalili mai kyau.

Ga masu hali da dama, musamman dattijai masu daraja irin su Alhaji Aminu Dantata, ana ganin hakan a matsayin karshe mai daraja a rayuwarsu ta duniya.

An birne Dantata a makabartar Baki'a a Madina

A wani rahoton, kun ji cewa an kammala jana'iza da birne Alhaji Aminu Alhassan Dantata a makabartar Baki'a da ke Madina.

A ranar Talata aka yi wa marigayin sallar jana'iza a masallacin annabi Muhammad SAW bayan Magariba.

Manyan mutane daga Najeriya da suka hada da gwamnoni, sarakuna, ministoci da sauransu sun halarci jana'izar dan kasuwan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng