Ondo: Gwamnati za Ta Binciki Abin da Ya Kashe Tsohon Gwamnan Jihar bayan kusan Shekaru 2
- Gwamnatin jihar Ondo ta bayyana cewa ta samu korafe-korafe daga mazauna Owo, mahaifar tsohon gwamna Rotimi Akeredolu
- Jama'ar na korafi ne kan zargin cewa akwai lauje a cikin nadi a kan rasuwar tsohon gwamnan da ya kwanta dama a shekarar 2023
- Gwamnati ta ce za ta fara binciken domin gano musabbabin rasuwar tsohon gwamna da ya sha fama da ciwon daji
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Ondo – Gwamnatin Ondo ta ce za a fara bincike domin gano abin da ya haifar da rasuwar tsohon gwamna Rotimi Akeredolu.
Tsohon gwamnan ya koma ga Mahalicci a ranar 27 ga Disamba, 2023, bayan ya sha fama da cutar daji.

Asali: Facebook
Jaridar Leadership ta wallafa cewa gwamnatin jihar ta bakin Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a, Kayode Ajulo, SAN, ta bayyana cewa ta karɓi koke daga wasu 'yan Ondo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu 'yan Ondo na son a binciki mutuwar Akeredolu
The Guardian ta ruwaito cewa gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne bayan wasu mazauna jihar da ke cikin damuwa sun miƙa ƙorafi ga Ma'aikatar Shari'a.
A cewar Ajulo, doka ta ba wa jama’a damar neman bayani idan akwai shakku ko rashin fahimta kan yadda wani ya rasu a jihar.
Ya ce:
“Ba laifi ba ne idan jama’a suka nemi a yi amfani da doka idan akwai damuwa da a kan wani al'amari."
“Antoni Janar na da alhakin daukar mataki bisa ka’ida idan irin wadannan damuwa sun taso daga jama’a.”
Jama'a sun yi korafi kan mutuwar Akeredolu
Ajulo ya tabbatar da cewa ma’aikatarsa ta karɓi ƙorafe-ƙorafe da dama daga kungiyoyi da kuma mutanen garin Owo, inda Akeredolu ya fito.
Sun bukaci a binciki abin da suka kira da kurakurai masu tada hankali da suka mamaye yadda Akeredolu ya rasu.

Asali: Facebook
A cewarsa:
“Mun karɓi koke daga kungiyoyi da dama cikin jihar da ma wajenta. Za mu bi duk wata hanyar doka. Dokar na nan don ta kare jama’a da tabbatar da gaskiya.
“Idan har akwai buƙatar kiran wani ko kama wani, za a bi matakin da ya dace.”
“Dole ne mu fuskanci wannan batu da ladabi, girmamawa da cikakkiyar girmamawa ga gwamnan da ya rasu da kuma zaman lafiyar jihar.”
Ya jaddada cewa akidar siyasa ko wani ra'ayi na son kai ba zai yi tasiri a kan binciken da ake kokarin gudanarwa ba a kan lamarin.
Tun bayan rasuwar tsohon gwamnan ne wasu ke ganin ko akwai hannu a ciki, duk da gwamnati ta fitar da sanarwa kan dalilin rasuwarsa a wancan lokaci.
Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu ya rasu
A baya, kun samu labarin cewa tsohon gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da wata doguwar rashin lafiya.
Marigayin ya rasu ne a hannun likitocin gwamnati da ke Legas a safiyar ranar Laraba. 23 ga watan Disamba, 2023 a lokacin yana zaɓaɓɓen gwamnan jihar Ondo.
Wasu rahotanni sun nuna cewa ya cika ne a yayin da ake ƙoƙarin kawo masa na’urar wanke koda zuwa inda ake kula da shi a boye, amma wasu sun ce ya rasu a Jamus.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng