Uba Sani Ya Aika da Sako ga Gwamnoni bayan Kisan 'Yan Daurin Aure a Plateau

Uba Sani Ya Aika da Sako ga Gwamnoni bayan Kisan 'Yan Daurin Aure a Plateau

  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya kai ziyarar ta'aziyya kan kisan da aka yi wa ƴan ɗaurin aure a Plateau
  • Uba Sani ya shawarci takwarorinsa gwamnoni da su kare ƴancin da ƴan ƙasa suke da shi na zuwa duk inda suke so
  • Gwamnan ya yabawa mutanen Basawa kan rashin ɗaukar doka a hannunsu sakamakon kisan gillar da aka yi wa ƴan uwansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi muhimmin kira ga takwarorinsa na sauran jihohin Najeriya bayan kisan da aka yi wa ƴan ɗaurin aure a Plateau.

Gwamna Uba Sani ya buƙaci gwamnonin da su mutunta ƴancin ƴan ƙasa na yin zirga-zirga cikin ƴanci kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) ya tanada.

Uba Sani ya ba gwamnonin Najeriya shawara
Uba Sani ya aika da sakon shawara ga gwamnoni Hoto: @ubasanius
Asali: Facebook

Gwamna Uba Sani ya yi wannan kiran ne yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai ƙaramar hukumar Kudan, inda ya jajanta wa iyalan matafiya 12 da aka kashe a Mangu, jihar Plateau, a hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Uba Sani ya kai ziyarar ta'aziyya

Yayin da yake jawabi ga al’ummar da lamarin ya shafa, Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyi shi ne mafi girman nauyin da kowace gwamnati ke da shi.

"Ko ɗan asalin jihar Kaduna ne ko daga wata jiha, muddin kana zaune a Kaduna, muna da nauyin kare rayuwarka da dukiyarka tare da tabbatar da zaman lafiya gare ka."

- Gwamna Uba Sani

Gwamnan wanda ya jagoranci wata babbar tawaga ta manyan jami’an gwamnati, ya yaba wa jama’ar Kudan bisa juriyar da suka nuna a yayin wannan mummunan lamari, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

"Ina yaba wa jama’a saboda ƙin ɗaukar doka a hannunsu. Wannan shi ne haƙiƙanin ruhin zaman lafiya da haɗin kai da muke fata a jihar Kaduna."

- Gwamna Uba Sani

Gwamnan ya bayyana cewa tun bayan faruwar lamarin, ya tura tawaga ƙarƙashin jagorancin sakataren gwamnatin jiha, Dakta AbdulKadir Mu’azu Meyere, domin ta jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa.

Haka kuma ya kai ziyara ga waɗanda suka tsira da rai da ke karɓar magani a asibitin 44 na rundunar sojojin Najeriya da ke Kaduna.

Uba Sani ya yabawa mutanen Basawa

Yayin da yake nuna godiya bisa zaman lafiya da fahimtar juna da ke yankin, Gwamnan ya yabawa shugabannin ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) da al’ummar Musulmi a yankin bisa haɗin gwiwarsu wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin addinai.

Uba Sani ya yaba mutanen Basawa
Uba Sani ya bukaci gwamnoni su kare 'yancin 'yan kasa Hoto: @ubasanius
Asali: Facebook

A matsayin wani ɓangare na ziyarar, Gwamna Uba Sani ya sanar da shirin gina hanyar da za ta haɗa Kudan da Basawa a ƙaramar hukumar Sabon Gari.

Haka kuma ya yi alƙawarin gina asibiti a Kudan domin ƙara tallafa wa al’ummar yankin.

An cafke waɗanda ake zargi da kisan ƴan ɗaurin aure

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Plateau ta tabbatar da cafke wasu da ake zargi kan kisan ƴan ɗaurin aure.

Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa ta cafke mutane 22 bisa zarginsu a hannu kan kisan da aka yi wa mutanen waɗanda suka fito daga Kaduna.

Hakazalika ta ƙara da cewa ta kai ragowar mutanen da suka samu raunuka sakamakon farmakin da aka kai musu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng