Koriya Ta Arewa za Ta Taimaki Shirin Makamin Nukiliya a Iran bayan Harin Isra'ila da Amurka
- Koriya ta Arewa ta caccaki Amurka da Isra'ila kan harin da suka kai wa Iran, inda ta ce wannan ya karya dokar kasa da kasa
- An dade ana zargin kasashen Iran da Koriya ta Arewa na hada kai a bangaren kera makaman yaki, musamman masu linzami
- Masana na ganin Koriya ta Arewa na iya taimaka wa Iran wajen sake gina wuraren kera makamai da jiragen Amurka suka lalata
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar North Korea – Koriya ta Arewa ta fitar da wata sanarwa a ranar Litinin inda ta nuna tsananin fushinta kan hare-haren da Amurka ta kai kan wasu cibiyoyin nukiliya na Iran.
Ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ta zargi Amurka da Isra’ila da haifar da tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar take hakkin kasashen.

Asali: Getty Images
Reuters ta wallafa cewa kasar ta bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga “yunkurin yaki mara dalili da kuma kokarin mamaye yankuna da Isra’ila ke yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce abin takaicin, shi ne yadda kasashen Turai suka rufe idanunsu, tare da mara wa Isra'ila baya tana ci gaba da harin zalunci a Gabas ta Tsakiya.
Iran da Koriya ta Arewa na kyakkyawar alaka
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa Iran da Koriya ta Arewa, wacce ke da makaman nukiliya, suna da dangantaka mai kyau tun shekaru da dama da suka gabata.
Haka kuma akwai zargin cewa suna hadin gwiwa a fannoni da dama na soja, daga ciki har da kera makamai masu linzami.
A cikin sanarwar da Koriya ta Arewa ta fitar, ta ce:
“Koriya ta Arewa na caccakar harin da Amurka ta kai wa Iran wanda ya take mutuncin yankin wata kasa mai cikakken iko da kuma muradun tsaronta.”

Asali: Getty Images
Ta kara da cewa:
“Ya kamata al’ummar duniya masu adalci su hade kai wajen kakkaɓe wannan mummunan aiki na Amurka da Isra’ila, tare da bayyana rashin amincewa da matakin da suka dauka.”
Koriya ta Arewa za ta taimaka wa kasar Iran
Wani kwamiti na kwararru da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa, wanda yanzu aka rusa, ya bayyana a shekarar 2021 cewa akwai alaka a tsakanin Koriya ta Arewa da Iran.
Kwamitin ya yi zargin cewa suna haɗin gwiwa don sake farfado da hadin gwiwarsu wajen kera makaman masu nisan zango.
Wani masani a cibiyar zaman lafiya ta kasa da kasa da ke Amurka mai suna Ankit Panda ya bayyana cewa:
“Pyongyang (babban birnin Koriya ta Arewa) na iya bayar da muhimmin taimako wajen sake gina cibiyoyin kera makaman Iran da aka lalata, ciki har da kirkirar sabbin wurare da za a boye su daga ido ko binciken kasa da kasa.”
Iran ta harbo jirgin sojojin Isra'ila
A baya, mun wallafa cewa rundunar sojin Isra’ila (IDF) ta tabbatar cewa an harbo ɗaya daga cikin jiragen leƙen asirinta a cikin ƙasar Iran yayin da yake shawagi.
Wannan lamari ya faru ne bayan hare-haren sama da dakarun Isra’ila suka kai kan muhimman cibiyoyin sojin Iran da ke yankin Yammacin ƙasar, musamman a lardin Kermanshah.
Isra’ila ta cikin wata sanarwa da ta fitar da safiyar Litinin ta ce jirgin da aka harbo ba shi da matuki, kuma babu fargabar cewa bayanai masu muhimmanci suna a hannun abokan gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng