Yaki Ya Cigaba: Iran Ta Harbo Jirgin Leken Asirin Kasar Isra'ila

Yaki Ya Cigaba: Iran Ta Harbo Jirgin Leken Asirin Kasar Isra'ila

  • Dakarun Iran sun harbo wani jirgin leƙen asiri mallakin Isra’ila a yankin Kermanshah da ke Yammacin Iran
  • Sojojin Isra’ila sun tabbatar da faruwar lamarin amma suka ce ba su da fargabar zubewar muhimman bayanansu
  • Rahotanni sun ce wannan shi ne karo na huɗu da aka harbo jirgin Isra’ila tun bayan fara harin soja kan Iran

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da cewa an harbo ɗaya daga cikin jiragen leƙen asirinsu a cikin ƙasar Iran.

Wannan na zuwa ne bayan da dakarun Isra’ila suka kaddamar da hare-haren sama kan cibiyoyin sojin Iran da ke Yammacin ƙasar, musamman a yankin Kermanshah.

An harbo jirgin Isra'ila a Iran
An harbo jirgin Isra'ila a Iran. Hoto Getty Images
Asali: Getty Images

Rahoton Jerussalam Post ya ce sanarwar da rundunar sojin Isra’ila (IDF) ta fitar da safiyar Litinin ya bayyana cewa jirgin da aka harbo ba shi da matuki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta kara da cewa Isra'ila ta ce ba su da wata fargaba game da yiwuwar zubewar bayanai ko sirri masu muhimmanci.

An harbo jirgin Isra'ila karo na 4

Times of Isra'el ta ruwaito cewa wannan shi ne jirgi na huɗu da aka harbo tun bayan fara farmakin da Isra’ila ke kai wa Iran.

A wani lokaci da ya gabata, sojojin Amurka sun harbo wani jirgin Isra’ila sakamakon kuskuren tantancewa a sararin samaniya, lamarin da ya janyo ɗan ce-ce-ku-ce a tsakanin kasashen.

Hare-haren da Isra’ila ke kai wa sun fi maida hankali ne kan cibiyoyin da ake zargin suna da alaƙa da shirye-shiryen nukiliya da kuma ajiya da kayan aikin soja na Iran.

Isra’ila na ci gaba da kai hari a Iran

Dakarun sama na Isra’ila sun sanar da kai wani sabon hari a ranar Litinin da safiya kan muhimman wuraren soja a yankin Kermanshah.

Wannan wani mataki ne da ke nuna cewa Isra’ila ba ta da niyyar sassauta farmakin da ta kaddamar bayan takaddamar soji da Iran.

Yankin Kermanshah da ke yammacin Iran ya kasance daya daga cikin wuraren da ake tunanin yana da muhimman sansanonin soji da kuma tashoshin da ke da alaƙa da harkokin leƙen asiri.

Bayanin Isra'ila kan harbo jirginta a Iran

Rundunar sojin Isra’ila ta jaddada cewa duk da fadowar jirgin a hannun abokan gaba, babu wani nau’i na bayani ko fasahar leƙen asiri da ke cikin jirgin da za a iya amfani da su.

Wannan sanarwar ta zo ne da nufin kwantar da hankulan jama’a da kuma kare martabar tsaro na ƙasar Isra’ila.

Ana cigaba da gwabza fada tsakanin Iran da Isra'ila
Ana cigaba da gwabza fada tsakanin Iran da Isra'ila. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Amurka ta roki China game da kasar Iran

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Amurka ta mika kokon bara ga China kan ta yi kokarin shawo kan Iran game da rufe hanyar ruwan Hormuz.

Bayan harin da Amurka ta kai Iran, majalisar kasar ta amince da rufe hanyar ruwan Hormoz a matakin ramako.

Binciken Legit ya gano cewa hanyar ruwan Hormuz na daga cikin manyan hanyoyin da ake bi wajen jigilar danyen mai a duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng