Yadda aka gano gawa da kawunan mutum uku a masai

Yadda aka gano gawa da kawunan mutum uku a masai

- Rundunar 'yan sandan jihar Ribas ta cafke wani kasurgumin mai garkuwa da Mutane mai suna Anthony Ndubuisi

- Ndubuisi kwararren mai kashe mutane ne bayan ya yi garkuwa da su, kuma ya amsa laifinsa bayan kama sa da aka yi

- Ya jagorancin jami'an tsaro inda ya nuna musu wata shadda da yake jefe gawawwakin wadanda ya kashe a gidansa

Rundunar 'yan sandan jihar Ribas ta damke wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane, Anthony Ndubuisi a karamar hukumar Umuebulu Etche ta jihar.

Wanda ake zargin dan asalin Ngo-Okpala ne da ke jihar Imo. An gano cewa yana da hannu a garkuwa da mutane tare da kashe wadanda ya kama da suka hada da bakin haure uku da wani dan Najeriya.

Kamar yadda jami'an tsaron suka bayyana, an yi nasarar kama shi sakamakon kokarin sashen yaki da garkuwa da mutane na Operation Sting bayan bayanan sirrin da suka samu.

Ndubuisi ya sanar da jami'an 'yan sandan cewa ya halaka wani mutum mai suna Ajumiene Offor. Ya yaudaresa daga Aba zuwa gidansa a kan wani kasuwanci da za su yi inda yayi garkuwa da shi tare da kashe shi a ranar 9 ga watan Yuni.

Bayan binciken, wanda ake zargin ya jagoranci jami'an tsaron zuwa gidansa da ke Umuebulu inda ya nuna musu wata masai da ke dankare da gawawwakin mutane.

Yadda aka gano gawa da kawunan mutum uku a 'shadda'
Yadda aka gano gawa da kawunan mutum uku a 'shadda'. Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnan Niger ya rage wa kansa da masu riƙe da muƙaman siyasa albashi

Bayan bude ta, jami'an tsaron sun samo kawunan mutum 3 da kuma gawa daya da ke rubewa ta wanda bai dade da kashewa ba. Tuni aka kwashesu zuwa ma'adanar gawawwaki.

Abubuwan da aka samo daga mai garkuwa da mutanen sun hada da bindigogi biyu da kuma harsasai masu rai, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

A yayin zantawa da manema labarai a ranar Talata a inda aka fidda gawawwakin, kwamishinan 'yan sanda, Joseph Mukan ya yi Allah wadai da al'amarin.

Amma kuma ya tabbatar da cewa yanzu suka fara yaki da mutane masu miyagun dabi'u a jihar.

Ya yi kira ga jama'a da su bude idonsu wurin sanin wadanda za su yi mu'amala da su don gujewa fadawa hannun mutanen banza.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel