‘Ba Maganar Nukiliya ba ne’: Sheikh Gumi kan Tsoron da Amurka Ke Yiwa Iran
- Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana cewa ba makamin nukiliya ne ke damun kasashen yamma ba, sai tsarin mulkin malaman addini
- Sheikh Gumi ya ce kasashen yamma suna kokarin rusa Iran ne saboda tsoron ikon da malaman addini ke da shi a irin wadannan kasashe
- Malamin ya zargi Amurka da kaddamar da hari kan Iran domin hana mulkin da ke kalubalantar ikon kasashen yamma da ke da karfi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana kan cigaba da kai ruwa rana tsakanin Iran da Isra'ila.
Sheikh Gumi ya tona asirin kasashen Yahuwdawa kan dalilin takurawa kasar Iran da suke yi a halin yanzu.

Asali: Facebook
Gumi ya yi tone-tone kan rikicin Iran/Isra'ila
Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani rubutu da ya yi a yau Lahadi 22 ga watan Yunin 2025 a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin rubutunsa, Sheikh Gumi ya ce mafi yawan kasashen kamar su Amurka da suka taso Iran a gaba duk ba maganar makamin nukiliya ba ne.
Sheikh Gumi ya ce suna tsoron mulkin malaman addini ne shiyasa suke fake wa da maganar mallakar makamin nukiliya.
A rubutun nasa, Malamin ya ce:
"Harin Amerika a kasar Iran:
"Sun sani sarai cewa Iran ba ta da nukilya, abun da suke so shi ne ruguza tsarin mulkin da malaman Addini ke jagora.
"Domin yafi nukiliya barazana, sun sani irin mulkin ne kadai ke hana mutane sujada garesu.
"Shi yasa ake kama malamai a wasu garuruwan domin tsoratar da su sanya baki a siyasa."
Wannan rubutu da ya yi ya jawo martanin daruruwan mutane wadanda mafi yawansu suka gaskata da kuma amincewa da abin da malamin ke zargi.

Asali: Getty Images
Shehi ya fadi silar gaba da Iran a duniya
Malamin ya ce a wurinsu wannan lamari ya fi mallakar makamin nukiliya hatsari shiyasa suka shiga damuwa.
Ya ce kwata-kwata ba su son mulkin malaman addini saboda ba za su samu su rusuna musu ba kamar yadda wasu ke yi musu wanda hakan ke kara musu karfin iko.
Sheikh Gumi na daga cikin malaman da suke yawan todfa albarkacin bakinsu musamman kan lamuran siyasar duniya.
Shehin ya yi kaurin suna wurin fadin albarkacin bakinsa daidai da abin da ya fahimta ko da kuwa ba zai yiwa mafi yawan jama'a dadi ba.
Assadus Sunnah ya magantu kan rikicin Ira, Isra'ila
Kun ji cewa Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya goyi bayan Iran kan rikicin da ke tsakaninta da Isra'ila, yana mai cewa nasararta za ta taimaki Musulunci.
Sheikh Assadus Sunnah ya ce duk Musulmin da ke fata Isra'ila ta doke Iran to akwai munafurci a zuciyarsa, yana kuma ganin hakan rashin kishi ne na addinin Musulunci.
Malamin ya bukaci Musulmai su tallafa da addu'a ko da ba da wani abu ba, yana mai jan hankalin su guji sabani saboda ra'ayi ko kungiyanci kan lamari da a yanzu ya sauya salo.
Asali: Legit.ng