Khamenei Ya Lissafo Malamai 3 da Za Su Gaje Shi a Iran, Ya Tsallake Sunan Dansa

Khamenei Ya Lissafo Malamai 3 da Za Su Gaje Shi a Iran, Ya Tsallake Sunan Dansa

  • Jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya zaɓi malamai uku da za su gaje shi idan aka samu matsala yayin yaki da Isra’ila
  • Rahoton ya ce Khamenei wanda yana cikin mafaka a karkashin kasa, ya cire ɗansa Mojtaba Khamenei daga jerin magadansa
  • Masana sun ce wannan mataki na nuna rashin hadin kai a cikin shugabannin Iran tare da tasirin siyasa a yankin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Babban jagoran Musulunci a kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya yi magana kan magajinsa a kasar.

Khamenei ya zabi malamai uku da za su iya gajonsa idan aka aka samu matsala yayin harin Isra’ila.

Khamenei ya fara maganar magajinsa a Iran
Ayatullah Khamenei ya zabi malamai 3 da za su gaje shi. Hoto: @khamenei_ir.
Asali: UGC

Khamenei ya magantu kan masu gadon kujerarsa

Rahoton bincike daga The New York Times ya bayyana haka ranar Asabar 21 ga watan Yunin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun bayyana cewa Khamenei mai shekaru 86, yana aiki daga mafakar ƙarƙashin ƙasa yayin da ake cigaba da fada.

An ce wasu “manyan jami’an Iran” sun tabbatar Khamenei ya yanke shawarar ne bayan jerin hare-haren kisan gilla da Isra’ila ta kai.

Abin lura a nan, ɗansa mai suna Mojtaba Khamenei, wanda ake tunanin zai gaje shi, ba ya cikin jerin mutanen da Khamenei ya zaɓa.

Wannan ya karya jita-jitar da aka dade ana yadawa cewa ana shirin yin gadon matsayin ta hanyar dangi a asirce.

Majiyar ta ce:

“Khamenei yana mafaka, ya naɗa malamai uku a maimakon ɗansa Mojtaba."
Ana tsaka da yaki, Khamenei ya jero magadansa
Ayatullah Ali Khamenei ya lissafo wadanda za su gaje shi. Getty Images.
Asali: AFP

Yadda ake zaben jagoran addini a Iran

Wasu majiyoyi suka ce Khamenei ya kuma zabi sababbin jagorori a rundunarsa ta soja, cewar rahoton Times of India.

Wannan mataki na nuna cewa yana shirin rasa manyan kusoshinsa idan Isra’ila ta ci gaba da kai farmaki.

A halin da ake ciki, yawanci ana zaben jagoran Iran ne ta hannun majalisar kwararru “Assembly of Experts” mai mambobi 88.

Amma abin da Khamenei ke yi na nuni da cewa yana son tsara abin da zai faru bayan mutuwarsa da kaucewa tsarin gargajiya.

Masana sun ce zaɓar mutane uku maimakon ɗaya yana nuni da rashin hadin kai da kuma gaggawa saboda haɗarin da ke gaba.

Duk da cewa ba a bayyana sunayensu ba, rahoton ya ce su ne waɗanda Khamenei ke da cikakken yarda da su.

Matakin zai iya tayar da ƙarin hatsaniyar siyasa a yankin musamman ganin yadda kasar Isra’ila ke kai farmaki a halin yanzu.

Wani jami’in leƙen asiri ya ce:

“Matakin Khamenei na nuna cewa Iran na shirin rasa shugabanta a tsakiyar yaki.”

A yanzu, sakon da ke fitowa daga Tehran yana nuna cewa Iran na shirin fuskantar sauyin shugabanci a wannan lokaci mai hatsari.

An yi hargitsi tsakanin Iran, Isra'ila a taro

Kun ji cewa an yi ce-ce-ku-kuce tsakanin jakadun kasashen Iran da Isra'ila a taron Majalisar ɗinkin duniya da aka yi a Amurka.

Jakadan kasar Iran, Amir-Saeid Iravani ya zargi Isra'ila da keta dokokin ƙasa da ƙasa a rikicin da ke faruwa a tsakaninsu.

Sai dai wannan kalamai ba su yi wa jakadan Isra'ila daɗi ba, wanda nan take ya maida masa martani da zafafan kalamai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.