Ana Ɓarin Wuta da Isra'ila, Shugaban Iran Ya Yi Magana da Shugaba Macron Ta Wayar Tarho
- Shugaban Faransa, Emmenuel Macron da takwaransa na kasar Iran, Masoud Pezeshkian sun tattauna kan rikicin da ke faruwa ta wayar tarho
- Macron ya ce shugaban Iran ya kira shi a waya kuma ya jaddada masa cewa bai kamata su dage cewa dole sai sun mallaki makamin nukiliya ba
- Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa ba ta da niyyar kera makaman nukiliya amma tana son ci gaba da nazari da bincike a kanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
France - Shugaban ƙasar Faransa da ke nahiyar Turai, Emmanuel Macron ya bayyana cewa ya tattauna da takwaransa shugaban Iran, Masoud Pezeshkian
Shugaba Macron ya ce sun tattauna kan muhimman batutuwan da suka shafi rikicin da ke faruwa a lokacin da shugaban Iran ya kira shi ta wayar tarho.

Asali: Getty Images
Emmanuel Macron ya bayyana duka abin da suka tattauna a wayar da suka yi a shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter yau Asabar, 21 ga watan Yuni, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An cigaba da ɓarin wuta tsakanin Iran da Isra'ila
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da faɗa ke ƙara tsanani tsakanin Isra'ila da Iran, lamarin da ya jawo asarar ɗaruruwan rayuka da dukiyoyi masu yawa.
Isra'ila ta fara tsokanar faɗa lokacin da ta kai hari kan cibiyar makamashin nukiliya ta Iran a ranar Juma'a, 13 ga watan Yuni, 2023, inda ta kashe manyan kwamndojin Iran.
Wannan hari na ba zata ya fusata Iran matuƙa, kuma nan take ta fara ɗaukar matakan ramuwar gayya ta hanyar kai hare-hare kan Isra'ila.
Tun daga wannan lokaci ƙasashen biyu ke ci gaba da musayar wuta har zuwa yau, Asabar, rana ta takwas kenan a jere.
Emmanuel Macron ya yi magana da shugaban Iran
Da yake bayyana abin da suka tattauna, Shugaban Faransa ya ce shi da Masoud Pezeshkian sun amince a ci gaba da tattauka na shirin nukiliya tsakanin Iran da ƙasashen Turai.
"Na jaddada masa cewa bai kamata Iran ta mallaki makaman nukiliya ba, kuma ya rataya a wuyanta ta bayar da tabbaci cewar manufofinta na zaman lafiya ne,” in ji Macron.
Shugaba Macron ya ƙara da cewa yana da tabbaci cewa akwai hanyar fita daga rikici da kuma kauce wa haɗurran da za su iya ƙaruwa.

Asali: Getty Images
Abin da shugaban Iran ya faɗawa Macron
A gefe guda, Shugaban Iran Pezeshkian, ya sake nanata cewa Iran ba ta da niyyar kera makaman nukiliya.
Sai dai ya shaidawa Shugaban Faransa cewa za ta ci gaba da bin hakkinta na amfani da makamashin nukiliya da zurfafa bincike a fannin.
An fallasa manufar Netanyahu kan Iran
A wani labarin, mun kawo maku cewa tsohon shugaban Amurka, Bill Clinton, ya ce da gangan Firaministan Isra'ilaz Benjamin Netanyahu ke yaƙar Iran don cimma burinsa.
Clinton ya ce ba komai ya sa Netanyahu ya ƙiƙiri faɗa da Iran ba sai don yana son ci gaba da mulkin ƙasar Isra'ila har abada.
Dattijon da ya bar ofis a 2001 ya buƙaci shugaban Amurka mai ci, Donald Trump ya kawo karshen wannan rikici domin kashe fararwn hula da mafit a ba ne.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng