'Yan Najeriya a Iran da Isra'ila Sun Shiga Tashin Hankali ana Ruwan Makamai
- Ƴan Najeriya da suka makale a Isra’ila da Iran sun nemi taimako daga mafakar ƙasa da suka fake yayin da ake cigaba da harba rokokin yaƙi
- Wasu daga cikinsu sun soki gwamnatin Najeriya bisa rashin yin gaggawar kwashe su kamar yadda ƙasashen duniya suka fara yi
- Gwamnatin tarayya ta ce tana jiran izinin ketare iyaka daga Armenia domin kwashe sama da ƴan Najeriya 1,000 daga yankunan kasae Iran
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tashin hankalin yaƙin da ke gudana tsakanin Isra’ila da Iran ya jefa 'yan Najeriya da ke zaune a ƙasashen biyu cikin mummunan hali.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan Najeriya sun shafe kwanaki suna fake a mafaka a ƙarkashin ƙasa domin tsira da rayukansu.

Asali: Getty Images
Wasu daga cikin su sun bayyana kokensu ta shafukan sada zumunta da kuma hira da jaridar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan Najeriya sun buya a karkashin kasa
Wani ɗan Najeriya da ke zaune a Tel Aviv, Ekene Abaka ya ce su na cikin mafakar ƙasa ne da sojojin Isra’ila suka tanada domin kare su daga hare-haren roka.
Wani injiniya ɗan Najeriya da ke zaune a birnin Urushalima ya ce yankin Tel Aviv ne mafi hadari inda galibin ƴan Najeriya ke zaune, kuma babu wani agaji daga gwamnati.
Ya kara da cewa ofishin jakadancin Najeriya da ke Tel Aviv ya rufe komai, wanda hakan ya kara dagula lamarin.
A cewarsa:
“Babu wani taimako daga gwamnati. Muna cikin mafakar ƙasa.”
'Yan Najeriya na gudu daga hare-haren Iran
Wani bidiyo da aka wallafa ya nuna ƴan Najeriya suna tsere cikin firgici yayin da Isra’ila ta sanar da shigowar rokokin Iran.
Rufe wasu daga cikin wuraren fakewa ya sa suka cigaba da gudu suna neman mafakar da ba a kulle ba.
Mai ɗaukar bidiyon ya ce gwamnati na tura saƙon gaggawa ga mazauna ƙasar mintuna 10 kafin roka ta faɗo.
An rufe makarantu da wuraren aiki a Isra’ila
Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila ta sanar da dakatar da dukkan ayyuka daga ƙarfe 8:00 na dare a ranar Lahadi.
Wannan matakin ya kara tsananta halin da ƴan Najeriya ke ciki a ƙasar, musamman ma masu sana’o’i da ɗalibai.
Gwamnatin Najeriya na jiran izinin kasar Armenia
A cewar Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya, an kammala shirye-shiryen jigilar ƴan Najeriya daga Tehran zuwa Armenia, inda za a ɗaukosu zuwa gida daga birnin Yerevan.
Sai dai har yanzu gwamnatin Najeriya na jiran izini da amincewar kasar Armenia don ketare iyakarta.

Asali: Twitter
Mai magana da yawun ma’aikatar, Kimiebi Ebienfa, ya ce an tanadi motocin daukar su, kuma ana ci gaba da tattaunawa da hukumomin Armenia don fitar da su cikin aminci.
An yi zanga zangar goyon bayan Iran
A wani rahoton, kun ji cewa mutanen kasar Iran sun yi zanga zangar adawa da Isra'ila a ranar Juma'a da ta gabata.
Mutanen kasar sun fito kan titunan kasar domin nuna goyon baya ga shugaban kasar su da cigaba da fafatawa da Irsa'ila.
Dubban mutane sun fito a wasu biranen duniya kamar kasashen Lebabon, Iraq da Yemen domin nuna goyon baya ga Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng