Martanin Iran kan 'Keta Mutuncin' da Trump Ya Yi Wa Fafaroma Leo

Martanin Iran kan 'Keta Mutuncin' da Trump Ya Yi Wa Fafaroma Leo

  • Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian ya soki kalaman Donald Trump kan jagoran ɗarikar Katolika, Paparoma Leo XIV
  • Donald Ttump ya fara cacar baki da Fafaroma, inda ya ce Leko XIV mai rauni ne wajen sha'anin laifi kuma bai dace da manufofin ketare ba
  • Fafaroma ya mayar da martani yana jaddada kira ga zaman lafiya da tattaunawa a maimakon yaki da zubar da jini

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Iran– Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi Allah-wadai da kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan Fafaroma Leo XIV.

Iran ta bayyana cewa waɗannan kalamai na Trump tamkar ya zubar da mutuncin jagoran Katolika tare da tauye darajar Yesu Al-Masihun da suke bi.

Iran ta soki shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian da na Amurka Donald Trump Hoto: Masoud Pezeshkian/Donald J Trump
Source: Getty Images

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Shugaban Iran ya mika saƙon goyon baya ga Fafaroma a madadin mutanen ƙasarsa tare da tir da Trump.

Kara karanta wannan

Duk da tsagaita wuta, Trump ya sake yin babbar barazana ga Iran

Abin da ya haɗa Trump da Fafaroma

A ranar Lahadi, 12 ga watan Afrilu, 2026, Trump ya bayyana cewa ba ya goyon bayan Fafaroma Leo, yana mai cewa shi mutum ne mai sassaucin ra’ayi kuma mai rauni wajen dakile laifi.

Ya kuma ƙara da cewa:

"Fafaroman ba shi da kwarewa a harkokin manufofin ƙasashen waje.”
“Mutum ne mai sassaucin ra’ayi, kuma ba ya yarda da dakile laifi."

Ya zargi Fafaroman da wasa da wata ƙasa da ke son mallakar makamin nukiliya, yana nuni da batun Iran, inda ya ce ba ya son Fafaroma da zai amince Iran ta mallaki makamin nukiliya.

Sai dai a ranar Asabar, Paparoma mai shekaru 70 ya yi kira ga shugabannin duniya da su kawo ƙarshen rikice-rikice.

Dangantaka ta yi tsaki tsakanin Leonda Trump
Martanin Iran kan Keta Mutuncin da Trump Ya Yi Wa Fafaroma Leo Hoto: Andrew Harnik/Vatican Pool/GettyImages
Source: Getty Images

A nasa ɓangaren, Pope Leo XIV ya mayar da martani ga kalaman Trump, yana mai cewa sakonnin Vatican na zaman lafiya da sulhu sun samo asali ne daga bishara, kuma ba ya tsoron gwamnatin Trump.

Kara karanta wannan

Abubuwa sun sukurkucewa Trump, ya sake yin rashin nasara a Amurka

Ya ce:

“Ba na tsoron gwamnatin Trump ko faɗar gaskiyar bishara, wadda na yi imani da ita. Wannan shi ne aikin da na zo yi, kuma wannan shi ne aikin coci. Mu ba ‘yan siyasa ba ne."

Martanin Iran ga Trump kan Fafaroma

A ranar Litinin, 13 ga watan Afrilu , 2026 Shugaban Iran ya mayar da martani, inda ya nuna goyon baya ga Fafaroman.

Ya ce:

“Mai alfarma Fafaroma Leo XIV, ina Allah-wadai da cin mutuncin da aka yi maka a madadin al’ummar Iran, kuma ina bayyana cewa cin mutuncin Annabi Isa, manzon zaman lafiya da ‘yan’uwantaka, ba abu ne da kowane mai ‘yanci zai amince da shi ba. Ina maka fatan ɗaukaka daga Allah."

Trump ya ba duniya mamaki

A baya, mun wallafa cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya dauki hankalin duniya da ya wallafa hoton kansa a irin wata shiga da ta yi kama da ta Yesu Almasihu.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Fafaroma Leo ya yi wa Trump zazzafan martani kan sukar shi

Hakan na zuwa ne sa'o'i bayan Trump ya caccaki Fafaroma Leo a wani dogon rubutu da ya yi yana cewa bai san harkokin kasa da kasa ba bayan ya nemi a daina yaki.

Alakar Trump da Fafaroma ta fara tsami ne tun bayan caccakar da Leo ke yi wa Amurka kan kai farmaki Iran da wasu kasashen duniya, wanda ya ce hakan bai dace ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng