An Samu Sabon Kakakin Majalisa da Mataimakinsa a Filato

An Samu Sabon Kakakin Majalisa da Mataimakinsa a Filato

  • A yayin da kakakin majalisar jihar Filato da mataimakinsa suka yi murabus, majalisar ta zabi sabon shugaba da mataimakinsa don ci gaba da jan ragamar majalisar
  • An nada Gabreil Dawang daga mazabar Pankshin ta Arewa a matsayin sabon kakakin majalisar, sai kuma Timothy Dantong daga mazabar Riyom matsayin mataimaki
  • Wannan sauyin da aka samu lokaci daya ba zai rasa nasaba da matakin Kotun Daukaka Kara na tsige Gwamna Caleb Mutfwang da wasu yan majalisar PDP ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Filato - Mamba mai wakiltar Pankshin ta Arewa a majalisar dokokin jihar Filato, Gabriel Dawang, a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, ya zama sabon shugaban majalisar.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun ɗauki mataki mai tsauri yayin da rikici ya tsananta a majalisar dokokin jihar PDP

Nadin sabon kakakin majalisar wanda dan jam’iyyar Young Peoples Party ne ya biyo bayan murabus din tsohon shugaban majalisar, Moses Sule, da mataimakinsa, Gwottaon Fom.

Kakakin majalisa da mataimakinsa
Majalisar jihar Filato ta yi sabon kakaki da mataimakinsa Hoto: @kc_journalist
Asali: Twitter

Timothy Dantong, mai wakiltar mazabar Riyom, shi ma ya zama sabon mataimakin kakakin majalisa, jaridar Tribune ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majalisar dokokin Filato da mataimakinsa sun yi murabus

Legit Hausa ta ruwaito maku yadda shugaban majalisar dokokin jihar Filato, Honorabul Moses Thomas, ya yi murabus daga mukaminsa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Haka nan kuma mataimakin shugaban majalisar dokokin, Honorabul Gwottaon Fom, ya bi sahunsa ya yi murabus daga kan kujerarsa mai lamba biyu a majalisar, Vanguard ta ruwaito.

An tattaro cewa wannan sauyin da aka samu lokaci daya ba zai rasa nasaba da matakin Kotun Daukaka Kara na tsige Gwamna Caleb Mutfwang da wasu yan majalisar PDP ba.

Kara karanta wannan

Ba bayin ka ba ne mu, sanatoci sun yi wa Akpabio rashin kunya kan dalili 1 tak, ya yi bayani

Gwamnan Filato ya dauki mataki bayan kotu ta tsige shi

A wani labarin, Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau, ya bayyana hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke na soke zabensa a matsayin koma baya na wucin gadi, Legit Hausa ta ruwaito.

Gwamnan ya sha alwashin cewa hukuncin ba zai hana shi mayar da jihar kan turbar zaman lafiya, hadin kai, da cigaba ba, kamar yadda jaridar Channels tv ta ruwaito a ranar Lahadi, 19 ga watan Nuwamba.

A ranar Lahadi, 19 ga watan Nuwamba Kotun dDaukaka Kara ta tsige Gwamna Mutfwang inda ta tabbatar da dan takarar APC, Nentawe Yilwatda a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben.

Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa, ya umurci tawagar lauyoyinsa da su shigar da kara a kotun koli.

Gwamnan ya bayyana matakin da zai dauka na gaba ta hanyar wata sanarwa da Gyang Bere, daraktansa na yada labarai da hulda da jama'a ya fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel